HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara
Fubara ya dawo ofis ne bayan Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da sanya a Jihar Ribas.
Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar.
- Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi
- ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba.
A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki a hukumance ga Gwamna Fubara.
Hotunan yadda magoyan suka taru: