HOTUNA: Yadda gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Kano
Hukumar ta ce tana gudanar da bincike domin gano musababbin tashin gobarar.
![HOTUNA: Yadda gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Kano HOTUNA: Yadda gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Kano](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/IMG-20250206-WA0025.jpg)
Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa.
Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin gona.
- An yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar NYSC Janar Tsiga
- Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai
Har ila yau, ta kashe shanu da sauran dabbobi mallakin mazauna ƙauyen.
Wasu daga cikin mazauna ƙauyen, Hayyo Zago da Abdulrahman Zago, sun ce gobarar ta ci gaba da ci har zuwa rana kafin jami’an kashe gobara su iss, inda suka yi nasarar kashe ta.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Jami’in Yaɗa Labarai na Yanki, Abdullahi Musa Gyadi-Gyadi, ya ce za a fitar da cikakken bayani kan asarar da aka tafka daga baya.
A nasa ɓangaren, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Amma ana tattara cikakken rahoto kan lamarin.
Go hotunan yadda gobarar ta yi ɓarna a ƙauyen: