HOTUNA: Yadda Musulmai ke murnar Mauludi a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu don gudanar da bikin Maulidi.

HOTUNA: Yadda Musulmai ke murnar Mauludi a Abuja

Al’ummar Musulmai na gudanar da tattaki don nuna murna da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (S.A.W) a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Tuni dai Musulmi suka shiga murna don tunawa da Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnatin Tarayya, yayin da ta ke taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar ranar, ta bukaci ’yan Najeriya da su kasance masu hakuri da juriya tare da koyi da kyawawan dabi’u na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Kazalika, Gwamnatin ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu don bai wa Musulmi damar gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar.