HOTUNA: Yadda Peter Obi ya yi buda baki da Musulmai a Kano

Dan takarar ya yi buda baki da Musulmai a Masallacin Triumph da ke Fagge.

HOTUNA: Yadda Peter Obi ya yi buda baki da Musulmai a Kano

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Kano, inda ya yi buda baki tare da al’ummar Musulmi a jihar.

Obi, ya ziyarci Masallacin Sheikh Jibril Umar Jibril wanda aka fi sani da Triumph da ke Karamar Hukumar Fagge a jihar.

Dan takarar shugaban kasar, ya shafe mintuna a masallacin bayan yin buda baki.

Ya ce: “Na zo ne domin yin buda baki tare da ku kuma ina farin cikin kasancewa a nan, na zo ba tare da nuna wariya ko la’akari da addini ko kabila ba.

“Ina fatan addu’o’in da muka yi a wannan wata na Ramadan mai albarka Ubangiji zai amsa mana, dukkaninmu ’yan Najeriya ne, kuma al’umma daya, na yi imani dole ne mu yi wa kasarmu addu’a.”

Tun da farko, Obi ya ziyarci Fadar Sarkin Kano, domin taya Sarkin da daukacin al’ummar jihar murnar fara azumin watan Ramadan.

Ga hotunan yadda ɗan takarar ya yi buda baki da Musulmai a jihar:

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana