HOTUNA: Yadda Rarara ya raba motoci da wayoyi a gasar wakar Tinubu

A ranar Asabar ce mawakin siyasar nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya yi bikin taron raba kyautuka ga wadanda suka lashe gasar waka da ya sa ka kan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. An gudanar da taron ne a birnin Katsina, kuma an gwangwaje wadanda suka […]

HOTUNA: Yadda Rarara ya raba motoci da wayoyi a gasar wakar Tinubu

A ranar Asabar ce mawakin siyasar nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ya yi bikin taron raba kyautuka ga wadanda suka lashe gasar waka da ya sa ka kan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

An gudanar da taron ne a birnin Katsina, kuma an gwangwaje wadanda suka yi nasara da kayatattun kyaututtuka.

Mutum shida ne suka samu kyautar motoci kirar Honda EOD, Sannan wasu 14 suka samu kyautar wayar samfurin IPHONE 13 PRO.

Kazalika, wasu mutum 200 kuma kowannensu ya samu kyautar 100,000. Ga kayatattun hotunan yadda bikin rarraba kyautuka ga matasan ya kasance.

Babban Bako Injiniya Muhatari Sagir Malumfashi da matashin da ya ci kyautar motar da kuma Dauda Rarar a lokacin bayar da kyautar. (Hoto: Asase)
Babban bako a taron bikin da kuma daya daga cikin matasan da suka ci kyautar mota. (Hoto: Asase)
Wani matashin da ya ji ci kyautar mota tare da manyan bakin da suka halarci taron (Hoto: Asase)
Dauda Kahutu Rarara yana mikawa daya daga cikin matasan 6 da suka ci kyautar mota a gasar (Hoto: Asase)
Honarabil Sani Danlami yana mika wa daya daga cikin matasan 14 da suka ci kyautar wayar Iphone ta sa kyautar. (Hoto: Asase)
Daddy hikima wanda a ka fi sani da Abale yana mikawa daya daga cikin matasa 100 wadanda suka ci naira kyautar 200,000 kowannensu (Hoto: Asase)
Daya cikin manyan bakin da suka halarci taron bikin na mikawa wata mace daga cikin matasan 100 da suka samu ta su kyautar 200,000 (Hoto: Asase)
Aisha Humaira na ba wa daya daga cikin matasan 14 da suka ci kyautar Iphone ta zamani (Hoto: Asase)
Injiniya Sagir Malumfashi yana mikawa daya daga cikin matasa 14 da suka ci kyautar Iphone tarer Dauda Rarara. (Hoto: Asase)
Baban Chinedu na mikawa daya daga cikin matasan ta sa kyautar ta wayar Iphone a yayin taron (Hoto: Asase)
Furodusa Bashir Maishadda na mikawa wani matashi daga cikin wadanda suka ci kyautar Iphone 13 ta zamani (Hoto: Asase)

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya