HOTUNA: Yadda Sarki Aminu Bayero ya yi Sallar Juma’a a Fadar Nassarawa
Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Sallar Juma’a a Babban Masallacin Kano.

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi sallar Juma’a a Fadar Nassarawa, inda ya shafe kusan mako guda yana zaman fada.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da dambarwa tsakanin Sarkin Sanusi II da Sarki Aminu Bayero da Gwamnatin Kano ta tuɓewa rawani a makon da ya gabata.
- An daure ta a kurkuku kan sayar da sabbin kudade
- Imanin Musulmi ba zai cika ba sai ya karɓi kowacce ƙaddara — Sarki Sanusi II
A ranar Juma’a ne aka samu rahoton cewa Sarki Aminu zai yi sallar Juma’a a Babban Masallacin Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi, zai yi tasa sallar, sai dai tuni rundunar ’yan sandan jihar ta yi watsi da rahoton.
Ga hotunan Aminu Bayero a masallacin Nassarawa: