Hotuna: Yadda Shugaba Buhari ya yi sallar Juma’a
Al’ummar Musulmi a wasu sassan Najeriya sun gudanar da sallar Juma’a a karo na farko bayan da gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da ta kafa da nufin hana yaduwar annobar COVID-19. Sai dai kawo yanzu akwai jihohi da dama da ba su kai ga ba da umarnin bude wuraren ibada ba. Amma […]
Al’ummar Musulmi a wasu sassan Najeriya sun gudanar da sallar Juma’a a karo na farko bayan da gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da ta kafa da nufin hana yaduwar annobar COVID-19.
Sai dai kawo yanzu akwai jihohi da dama da ba su kai ga ba da umarnin bude wuraren ibada ba.
Amma a jihohin da aka ba da umarinin yin haka an samu sauye-sauye a wasu masallatan Juma’a, inda akasari aka sanya takunkumin rufe baki da hanci.
- HOTUNA: Yadda Sallar Idi ta gudana a sassan Najeriya
- Hotuna: Yadda aka yi Idi a gidan Dahiru Bauchi da wasu jihohin Najeriya
A wasu masallatan an ba da tazara; yayin da hakan ya kasa samuwa a masallatai da dama da wakilin Aminiya ya ziyarta.
Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tasa sallar ta Juma’a a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ga kuma hotunan yadda ta kasance.