Fagen SiyasaHotuna• Created May 20, 2022 08:08
HOTUNA: Yadda Tinubu ya samu kyakkyawar tarba a Kano
Tinubu ya samu tarba mai kyau daga gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Ganduje.
Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ya ke wa Tinubu maraba da sauka
Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu kyakkyawar tarba a yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano don ganawa da wakilan jam’iyyar a jihar.
Ga hotunan ziyarar tasa ta ranar Alhamis, 19 ga Mayu, 2022:
Tinubu a lokacin da ya sauka a Filin Firgin Sama na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano
Hadimin Shugaban Kasa Buhari kuma mai neman takarar dan Majalisar Tarayya a mazabar Gaya, Bashir Ahmad.
’Yadda masu rawan Koroso suka kayatar a lokacin da aka tarbi Tinubu a Kano.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da wasu jagororin APC a Kano
Ganduje tare da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma Sanata Barau
Tinubu a tsakanin magoya bayansa a lokacin ziyarar da ya kai Kano ranar Alhamis.
Wasu ’yan jam’iyyar APC na Jihar Kano a lokacin da Tinubu ya ziyarci jihar.
Mutane sun yi cincirindo, babu masaka tsinke a lokacin Tinubu ya kai ziyara Kano.
Dandazon mutane da suka halarci taron tarbar Tinubu a Kano.