HOTUNA: Yadda Uba Sani ya yi bankwana da ɗaliban Kuriga
Gwamnatin ta miƙa su ga iyayensu bayan kubutar da su a ranar Lahadin da ta gabata.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya sake karbar bakuncin ɗaliban Kuriga da ‘yan bindiga suka sace, inda ya yi bankwana da su lokacin da suke shirin komawa gida.
Gwamnan ya tarbe su ne a gidan gwamnatin jihar da ke Kaduna, bayan sun shirya domin komawa wajen iyayensu.
Sai dai tun da fari iyayen daliban sun yi korafin rashin komawar yaran wajensu, amma gwamnatin jihar ta bayyana cewar ana duba lafiyarsu ne.
Da yammacin ranar Alhamis ne, Gwamna Sani ya sake yin wani zama da ɗaliban, kafin daga bisani aka sanya su cikin motoci bas-bas domin kai su gida.
Motocin sun tashi tare da rakiyar jami’an tsaro zuwa kauyensu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Ga hotunan a ƙasa: