HOTUNA: Yadda zamanantar da sana’ar zayyana ya kai ga kafa mata makaranta a Kano
Yanzu dai an zamanantar da wannan sana’ar, ta tashi daga ta gargajiya
A da, an fi sanin zayyana watau adon zane-zane da ake yi wa allon da ake ba masu saukar karatun Al-Kurani a makarantun tsangaya da Islamiyyu, amma yanzu wannan sana’ar ta bunkasa a jihar Kano.
Bunkasar sana’ar ta samu ne ta hanyar zamanantar da yanayi da tsarinta da kuma yin ta a wurare daban-daban kamar fatoci, da takarda, da bango da kuma sauran wurare domin ya kayatar.
- Ana zargin Boka da yi wa matar aure ciki a Bauchi
- Masu garkuwa sun sako tsohon Kansila, sun ba shi kyautar babur don ya tara musu N8m
Hakan ya kai ga kafa wata makarantar da ake koyar da wannan fasaha ga matasa maza da mata masu sha’war koyon zane ta fasahar zamani, mai suna Gabari Institute of Islamic Calligraphy And Geometric Design a Kano.
Ga wasu daga cikin kayatattun hotunan wannan ci gaban fasahar zayyana a zamanance.