Dandalin nishadiHotuna• Created June 8, 2023 21:30
HOTUNA: ‘Yan Kannywood sun ziyarci Buhari da Aisha a Daura
HOTUNA: ‘Yan Kannywood sun ziyarci Buhari da Aisha a Daura
Wasu daga cikin fitattun ‘yan masana’antar Kannywood sun kai ziyara ga uwargidan tsohon Shugaban Kasa Aisha Muhammadu Buhari a garin Daura.
Ziyarar ta wasu daga cikin gamayyar kungiyoyin da suka yi aiki da ita ne a shirinta na ‘FUTURE ASSURED’ a inda suka rarraba wa mata da yara kanana da kuma gajiyayyu kayayyaki daga ofishin na tsohuwar ‘First Lady’, da daidaikun kungiyoyinsu.
Marubuciya Fauziyya D. Suleiman da Jaruma Rashida Adamu Mai Sa’a da dauke da takardar yabo kafin su ba Uwargida Aisha Buhari HOTO: Image Palace Photography
Shugabar marubutan shirin Dadin Kowa na Arewa24 Zuwairiyya Girie da jaruma Fauziyya Mai kyau da Mansura Isah da kuma Anti Bebi da takardrar yabon uwargida Aisha Buhari HOTO: Image Palace Photography
Rashida Adamu da Mansura Isah tare da tsohon shugaba Muhammadu Buhari da Uwargidansa Aisha a yayin mika mata takardar yabon HOTO: Image Palace Photography
Uwargida Aisha Buhari yayin tarbar masu ziyarar ‘yan kannywood da sauran shugabannin ‘yan kungiyoyin HOTO: Image Palace Photography
Muhammadu Buhari na yaba tasa kyautar da masu ziyarar suka yi masa tare da Rashida Mai Sa’a da kuma daya da cikin shugabannin kungiya. HOTO: Image Palace Photography
Marubuciya Fauziyya D. Suleiman tare da Uwargida Aisha Buhari bayana kammala ziyarar. HOTO: Image Palace Photography
Marubuciya Zuwaira Girie tare da uwargida Aisha Buhari bayan kammal ziyarar HOTO: Image Palace Photography
Jarumin barkwanci Baba Ari da tare da sauran ayarin masu ziyarar a Rijiyar Kusugu mai tarihi bayan kai ziyarar ga tsohon Shugaban Kasa HOTO: Image Palace Photography