HOTUNA: ’Yan Tijjaniya sun yi taron zikiri a Fadar Nassarawa

Sayyadi Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ne wakilin ’yan Tijjaniyar a yayin taron zikirin da aka gudanar.

HOTUNA: ’Yan Tijjaniya sun yi taron zikiri a Fadar Nassarawa

’Yan ɗariƙar ƙarƙashin jagorancin Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman sun gudanar da taron zikirin shekara a Fadar Nassarawa da ke Jihar Kano.

An dai sabon gudanar da zikirin na shekara-shekara a duk makon ƙarshe na ƙarshen shekarar Musulunci ta Hijiriya.

Majalisar Ƙoli ta Ɗariƙar Tijjaniya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ce ke gudanar da zikirin domin neman agajin Allah kan tabbatar da aminci da wanzuwar ƙasar nan.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sayyadi Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ne wakilin ’yan Tijjaniyar a yayin taron zikirin da aka gudanar wannan Juma’ar a Birnin Dabo.

’Yan Tijjaniya daga jihohin Kebbi, Sakkwato, Bauchi, Gombe, Zaria, Yobe da sauransu sun halarci taron zikirin.

A shekarun da suka gabata dai, Shugaban Darikar Tijjaniya na Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yakan nemi amincewar Sarkin Kano na 13, marigayi Ado Bayero, dangane da taron zikirin da kuma yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane watan Muharram — wata na farko a kalandar Musulunci.

Marigayi Sarki Ado yakan aike da saƙon gayyata zuwa ga sauran malaman Tijjaniya kuma tun daga wancan lokaci ya zama al’adar da ake gudanarwa duk ƙarshen shekara domin inganta alaƙa a tsakanin Musulmi.

Hotunan zikirin Tijjaniya na shekara-shekara daga Fadar Nassarawa:

 

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom