HOTUNA: Zanga-zanga ta barke a Kano kan soke nasarar Abba Gida-Gida
A baya irin haka ta haifar da yamutsi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar.
An wayi gari masu zanga-zanga sun mamaye titunan Kano domin sake nuna rashin dadinsu kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kan gwamnan jihar.
A makonnin da suka gabata ne Kotun Daukaka Kara ta kori Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, inda ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na bana.
- Kotun Daukaka Kara ta kori Kakakin Majalisar Nasarawa
- Kotu ta tabbatar wa Kefas Agbu na PDP kujerar Gwamnan Taraba
Rashin gamsuwa da hukuncin ne masu zanga-zangar tun da misalin ƙarfe takwas na safiyar wannan Larabar suka mamaye wasu manyan tituna a jihar ciki har da karkashin babbar gadar Kofar Nassarawa da titin Maiduguri daidai gadar kasa ta Muhammadu Buhari.
Sai dai akwai jami’an tsaro a tare da masu zanga-zangar da ke cikin shirin ko ta kwana.
Masu zanga-zangar na rera wakoki da Hausa, “Ba za mu yarda ba, ba za mu yarda ba, Kano ta Abba ce, a dawo mana da hakkinmu a fallasa zaluncin kotu.”.
Aminiya ta ruwaito cewa a baya-bayan nan an yi irin wannan zanga-zangar a lokuta daban-daban a babban birnin, inda aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.
A halin da ake ciki, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Kano ta gargadi mutane ko gungun jama’a da su guji zanga-zanga kan hukuncin kotun.