HOTUNA: Ziyarar Sarki Sunusi II a taron Majalisar Dinkin Duniya

Ya yi wata ganawa ta musamman da Amina Mohammed, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

HOTUNA: Ziyarar Sarki Sunusi II a taron Majalisar Dinkin Duniya

Halifan Tijjaniya kuma Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi na II na wata ziyara birnin New York ta Amurka a bisa a gayyatar Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar ta gayyace shi ne domin halartar wani taro na musamman kan Cimma Muradun Karni SDG, a inda Halifan ya gabartar da jawabi kan ilimi.

Ya kuma gana da wasu manyan mutanen aka gayyata daga sassa na duniya domin halartar taron.

Kazalika, ya yi wata ganawa ta musamman da Amina Mohammned, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar a ofishinta

Ga yadda ziyarar ta wakana a cikin hotuna:

Muhammadu Sunusi a yayin ganawarsu da Mataimakiyar Babban Sakataren MDD, Amina Mohammed a ofishinta da ke shalkwatar Majalisar (Hoto: Al Ameen)
Muhammadu Sunusi na II tare da Ministar Kudi, Zainab Ahmed a zauren taron (HOTO: Al Ameen)
Muhammadu Sunusi na II tare da daga cikin wadanda aka gayyata a taron (Hoto: Al Ameen)
Muhammadu Sunusi na II tare da wasu daga cikin manyan bakin da aka gayyata a taron (Hoto: Al Ameen)
Muhammadu Sunusi na II tare da wasu daga cikin wadanda aka gayyata a taron (Hoto: Al Ameen)
Khalifa Muhammadu Sunusi na II tare da wadanda aka gayyata a taron (Hoto: Al Ameen)
Sarkin Kano na 14 a yayin zaman taron na musammam kan ilimi, shi da wadanda suka halarci taron a shalkwatar MDD (Hoto: Al Ameen)
Khalifa a yayin wani zaman taron a shalkwatar MDD (Hoto: Al Ameen)

Aminiya ta ruwaito, a ranar Laraba Majalisar Dinkin Duniyar za ta yi taronta na shekara-shekara, karo na 77 da za a gudanar a birnin New York.