Hotunan bikin bajekolin fina-finai a Saudiyya

Kayatattun hoton bikin baje kolin fina-finai na farko bayan sauye-sauyen da Yari Jiran Gado, Mohammed bin Salman ya yi daga shekarar 2017

Hotunan bikin bajekolin fina-finai a Saudiyya

Meredith Mickelson daga Amurka tare da Shugaban Taron bajekolin, Mohammed al Turki a lokacin da ta isa wurin taron (PATRICK BAZ Red Sea Film Festival)

A karon farko a gudanar da taron baje kolin fim a kasar Saudiyya inda jarumai daga Amurk da Faransa da kasashen larabwa da sauran sassan duniya suka halarta.

Fina-finai 168 cikin harsuna 30 ne aka hasa taron, mai suna ‘Red Sea Film Festival’, wanda ya gudana a birnin Jidda.

Ga kadan daga hotunan taron:

Alessandra Ambrosio na daukar hoto a lokacin taron baje kolin fina-fanan mai suna Red Sea Film Festival. (Hoto: Getty Images).
Meredith Mickelson daga Amurka tare da Shugaban Taron bajekolin, Mohammed al Turki a lokacin da ta isa wurin taron ranar Litinin 6 ga watan Disamba, 2021 a birnin Jidda na kasar Saudiyya. (Hoto: Red Sea Film Festival).
Jaruma kuma furodusa a Hollywood, Hilary Swank a lokacin bude taron ranar 6 ga watan Disamba, 2021. (Hoto: Red Sea Film Festival).
Furodusa mace daga Saudiyya Haifaa al Mansour a ta karbi kyautar karramawa a lokacin bude taron. (Hoto: Red Sea Film Festival).
Jarumi Vincent Cassel daga Faransa tare da Tina Kunakey suna daukar hoto. (Hoto: Red Sea Film Festival)
Mayssa Maghrebi, jarumar fim daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasar da Moroko, a lokacin taron baje kolin fina-finan. (Hoto: Red Sea Film Festival).
Candice Swanepoel na daga cikin mahalarta kasaitaccen taron da aka haska fina-finai daban-daban cikin harsuna 30 a kasar Saudiyya. (Hoto: Arab News).
Jaruma Leila Eloui daga kasar Masar a wurin babban taron baje kolin fina-finan a ranar Litinin. (Hoto: Red Sea Film Festival).

Jarumar fina-finan Larabawa, Shanina Shaik a wurin taron. (Hoto: Arab News).

DJ Chantel Taleen Jeffries, daga kasar Amurka, a wurin taron na Red Sea Film Festival. (Hoto: Red Sea Film Festival).
Hoto: Arab News