Hotunan jana’izar kwamandan sojin Najeriya da Boko Haram ta kashe

A ranar Litinin 21 ga Satumba, 2020, Allah Ya yi wa Kanar Dahiru Chiroma Bako cikawa sakamakon raunin harbi da ya samu a wata musayar wuta tsakanin dakarun sojin Najeriya da mayakan Boko Haram a Damboa, Jihar Borno. Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka yi jana’izarsa ranar Talata a Barikin Sojoji na Maimalari da […]

Hotunan jana’izar kwamandan sojin Najeriya da Boko Haram ta kashe

A ranar Litinin 21 ga Satumba, 2020, Allah Ya yi wa Kanar Dahiru Chiroma Bako cikawa sakamakon raunin harbi da ya samu a wata musayar wuta tsakanin dakarun sojin Najeriya da mayakan Boko Haram a Damboa, Jihar Borno.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka yi jana’izarsa ranar Talata a Barikin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri.

Babban Hafson Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai yana mika wa matar marigayi Kanal Dahiru Chiroma Bako tutan Najeriya bayan binne mamacin a ranar Talata.
Gwamnan Borno, Babagana Zulum da shudayen kaya, sa Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Burata (a tsakiya) da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rundunar Sojin Kasa, Sanata Ali Ndume a yayin sallar jana'izar
Gwamnan Borno, Babagana Zulum (da shudayen kaya), Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Burata (a tsakiya sanye da kayan sojoji) da kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rundunar Sojin Kasa, Sanata Ali Ndume a yayin sallar jana’izar.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum a lokacin da yake jawabi a taron jana’izar mamacin. A lokacin jawabin gwamnan ya yi alkawarin tallafin Naira miliyan 20 da kuma gida ga iyalan marigayin. (Hoto: New Media).
Sojoji sun sanya gawar mamacin a tsakiya za su dauke ta gabanin a sanya mamacin a makwancinsa.
Gawar marigayi Kanar Dahiru Ciroma Bako lullube da tutar Najeriya a wurin da aka sallace ta.
Limamin soji ne ya jagoranci sallar jana’izar marigayi Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka yi a Barikin Sojoji na Maimalari.