Aminiyar KurmiHotunaTa'aziya• Created December 26, 2020 09:17
Hotunan Jana’izar Sarki Sani Kabiru na Legas
Ranar Alhamis 24 ga watan Disamba, 2020 da dare Allah Ya yi wa daya daga cikin sarakunan Jihar Legas, Sarki Sani Kabiru rasuwa. Sarki Sani Kabiru ya rasu yana da shekara 57 bayan ya yi fama da jinya, an kuma yi masa sutura a ranar Juma’a a Makabartar Hausawa ta Morkaz da ke unguwar Agege […]
Ranar Alhamis 24 ga watan Disamba, 2020 da dare Allah Ya yi wa daya daga cikin sarakunan Jihar Legas, Sarki Sani Kabiru rasuwa.
Sarki Sani Kabiru ya rasu yana da shekara 57 bayan ya yi fama da jinya, an kuma yi masa sutura a ranar Juma’a a Makabartar Hausawa ta Morkaz da ke unguwar Agege a Legas.
Shaikh Tijjani Imam Khalifan Tijjaniya na Legas ne ya jagoranci jana’izar wadda kwamishinan Albarkatun Ruwa na Legas Alhaji Ahmad Kabir ya halarta.
Aminiya ta kawo maku hotunan yadda aka yi jana’izar sarki Sani Kabiru.
Sashe na mahalarta jana’izar a lokacin da ake binne sarkin.
Shaikh Tijjani Imam, Khalifan Tijjaniya na Legas a lokacin da ya jagoranci jana’izar
Wasu mahalarta jana’izar suna sauraron wa’azi daga malamai
Wani sashe na mahalarta jana’izar a ranar Juma’a a Legas
‘Yan Majalisar Sarkin Hausawan Agege a lokacin da suke karbar gaisuwar ta’zziyya.
Sarkin Hausawan Agege Alhaji Muhammadu Musa Dogonkadai yana karbar gaisuwar ta’aziyya.
Daga dama Sarkin Hausawan Agege Alhaji Musa Dogonkadai da Sarkin Hausawan Idiyarba Alhaji Hassan Auyo suna yi wa marigayi Sarki Sani Kabiru Addu’a.
Gawar Sarki Sani Kabiru a lokacin da aka sanyata a Kabari
Daga tsakiya Kwamishinan Albakacin Ruwa na Jihar Legas, Akitet Ahmad Kabir a lokacin jana’izar.
Wani sashe na mahalarta jana’izar da aka gudanar ranar Juma’a a makabarta.