Hotunan matsahin hafsan sojin da ya rasu a hatsarin jirgin Kaduna
Tuni aka yi jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.
An gano daya daga cikin hafsoshin Sojin Saman Najeriya da suka rasu bayan jirginsu ya yi hatsari a ranar Talata.
Daya daga cikinsu shi ne Abubakar Alkali, dan asalin Jihar Yobe ne, kuma ya kwanta dama ne bayan jirgin da shi da abokin aikinsa suke tukawa ya fadi a Sansanin Sojin Sama da ke Kaduna.
Ga wasu daga cikin hotunan Abubakar wanda tuni aka yi jana’izarsa bisa tsarin Musulunci: