Jama’a ke hawa dutsunan Dala da Goron Dutse da sauran abubuwa na sada zumunci da ibabada da sauransu.
A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba a ka yi bikin ranra Takutaha, wadda ake murna a matsayin ranar bakwai bayan Mauludin Manzon Allah (SAW).
Ga wasu hotunan yadda ranar ta kasance a Kano, inda jama’a ke hawa dutsunan Dala da Goron Dutse da sauran abubuwa na sada zumunci da ibabada da sauransu.
Hotuna: Abba Adamu.
Dandazon wasu mata a cikin garin Kano a lokacin bikin Takutaha a ranar Laraba 5 ga Oktoba, 2023. (Hoto: Abba Adamu).Masu bikin takutaha a lokacin da suke hawa Dutsen Dala a ranar Takutaha a Kano. (Hoto: Abba Adamu).Masu tattakin bege a ranar Takutaha ta shekarar 2023 a birnin Kano. (Hoto: Abba Adamu).Yadda mutane suka yi dafafi suna tattaki a birnin Kano a ranar Takutaha a Kano, ranar Laraba 4 ga Oktoba, 2023. (Hoto: Abba Adamu).Motar DJ da masu begen Manzon Allah (SAW) a yayin tattaki ranar Takutaha a Kano. (Abba Adamu).