Hotunan yadda aka gudanar da addu’o’i kan matsin rayuwa a Kano
An gudanar da addu’o’in duk da kiran a dakata saboda dalilai na tsaro.
An gudanar da taron addu’o’i kan matsin rayuwa a wasu sassa daban-daban na Jihar Kano da ke Arewacin Nijeriya.
Wannan na zuwa duk da kiraye-kirayen dakatar da gudanar da addu’o’in na ƙasa da aka shirya somawa yau Asabar saboda dalilai na tsaro.
- Poland ta roƙi Nijeriya ta saki ’yan ƙasarta da suka ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga
- Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 a wata makaranta a Gaza
Aminiya ta ruwaito cewa an yi taron addu’o’in ne a Masallacin Isiyaku Rabiu da ke Unguwar Goron Dutse a Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano.
Cikin wani saƙo da wani mai suna Rabiu Sharma ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an yi saukar karatun al-Qur’ani da addu’o’i a Masallacin Khalifa Isiyaka Rabiu domin Allah Ya kawo sauƙi kan yanayin ƙuncin rayuwa da aka tsinci kai a ƙasar a halin yanzu.
A bayan nan dai an gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa wadda kuma daga bisani ta rikide ta zama tarzoma, inda aka riƙa ƙone-ƙone, kashe-kashe da sace-sacen da kuma lalata dukiyoyin gwamnati da na al’umma.
Mafi shara daga cikin unguwanni da wuraren da aka gudanar da salloli da addu’o’in sun haɗa da Yankaba, Daurawa, Gyadi-Gyadi, Hausawa, Sabon Titi, Panshekara da Tudun Murtala.