Hotunan yadda dalibai suka koma karatu a Kaduna da Kano

Ga hotunan yadda wasu makarantun sakandare a jihohin Kaduna da Kano suka ci gaba da karatu a ranar Litinin bayan dage dokar kulle sakamakon bullar annobar COVID-19:

Hotunan yadda dalibai suka koma karatu a Kaduna da Kano

Wani dalibi ke nan lokacin da yake wanke hannu kafin shiga aji don daukar darasi a Kwalejin Sarduna Memorial College a Kaduna.

Ga hotunan yadda wasu makarantun sakandare a jihohin Kaduna da Kano suka ci gaba da karatu a ranar Litinin bayan dage dokar kulle sakamakon bullar annobar COVID-19:

Wasu dalibai ke jiran daukar darasi a cikin aji a Kwalejin tunawa da Sardauna (SMC) da ke Kaduna ranar Litinin.
Dalibai mata kafin su fara daukar darasi a makarantar sakandaren gwamnati ta Maimuna Gwarzo da ke Kaduna.
Wasu dalibai da ke shirin shiga azujuwansu a ranar da aka bude makarantu a Kaduna.
Wasu dalibai ke shirin shiga azujuwansu don daukar darasi a Kwalejin Sarduna Memorial College a Kaduna.
Wasu dalibai ke nan a lokacin da suke wanke hannu kafin shiga aji don daukar darasi a SMC, Kaduna.
Wasu daliban makarantar sakandaren gwamnati ta Maimuna Gwarzo a Kaduna, ke daukar ruwa zuwa ajinsu lokacin daukar darasi.
Wasu dalibai ke nan a matarantar ‘yan mata ta Shekara da ke Kano
Yadda ake nome ciyayi a makarantar ‘yan mata ta Shekara da ke Kano bayan komawar dalibai.