Hotuna: Yadda wasu Makafi ke sana’ar nika
Wasu magidanta ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da makanta sun bayyana cewa bara kaskanci ne don haka suka rike sana’ar nika garin albo. Magidantan uku, masu shekaru daga 60 zuwa 54 mazauna garin Ago-Aare, Jihar Oyo, sun shaida wa Aminiya cewa cutar makantar ta same su ne a lokacin da suke cika shekaru […]
Wasu magidanta ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da makanta sun bayyana cewa bara kaskanci ne don haka suka rike sana’ar nika garin albo.
Magidantan uku, masu shekaru daga 60 zuwa 54 mazauna garin Ago-Aare, Jihar Oyo, sun shaida wa Aminiya cewa cutar makantar ta same su ne a lokacin da suke cika shekaru 30 a rayuwarsu.
Babban su mai suna Muhammadu Sa’adu Isiyaka ya ce kaninsa Sulaiman Isiyaka wanda ke sana’ar dabbobi, shi ne ya sayi injin nika garin alabo wanda yanzu suke amfani da shi a sana’ar da suke dogaro da ita.
Aminiya ta dauko muku hotunan makafin uku da yadda suke sana’ar su ta mika garin albo.