Hotunan ziyarar Akon zuwa Zawiyyar Shaikh Ibrahim Nyass
Shahararren mawakin duniya dan asalin kasar Senegal da ke zaune a Amurka Akon, ya ziyarci Zawiyyar Fitaccen Shehun Malamin Islama Shaikh Ibrahim Nyass Kaulaha, da ke kasar Sanegal. A ‘yan kwanakin nan tauraron na wakokin R&B wanda sunansa na asali Alioune Badara Thiam ya kudiri aniyar gina katafaren birni a kasar Sanegal domin farfadowa da […]
Shahararren mawakin duniya dan asalin kasar Senegal da ke zaune a Amurka Akon, ya ziyarci Zawiyyar Fitaccen Shehun Malamin Islama Shaikh Ibrahim Nyass Kaulaha, da ke kasar Sanegal.
A ‘yan kwanakin nan tauraron na wakokin R&B wanda sunansa na asali Alioune Badara Thiam ya kudiri aniyar gina katafaren birni a kasar Sanegal domin farfadowa da bunkasa al’adun Afirka a tsakanin ‘yan Nahiyar mazauna Turai; Aikin da yac e zai lakume Dalar Amurka biliyan shida.
Kungiyar matasan Darikar Tijjaniya ta Fityanul Islam ce ta sanya hoton ziyarar da Mawaki Akon ya kai Zawiyyar a shafin ta na sada zumunta: