Huɗubar Annabi (SAW) ta Ban-Kwana

Mun shaida lallai ne kai ka bayar da amana, kuma ka isar da sakon kuma ka yi nasiha.

Huɗubar Annabi (SAW) ta Ban-Kwana

Wannan Huduba Shugabanmu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ta ce a ranar 9 ga watan Zul-Hajji, shekara ta 10 Bayan Hijira daidai da shekara ta 632 Miladiyya a Dutsen Arfa, yau Asabar shekara 1435 cif ke nan da gabatar da wannan huduba.

Kuma ita ce huɗubarsa ta ƙarshe ga ɗimbin Musulmin da suka fito daga sassan duniya kuma suka halarci Aikin Hajji tare da shi a Hajjinsa na karshe:

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba gare Shi.

Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi.

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, mulki naSa ne kuma godiya taSa ce, Yana rayawa, Yana kashewa, kuma Shi a kan dukkan komai Mai iko ne.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, Ya cika alkawarinSa, Ya taimaki bawanSa, kuma ya ruguza rundunoni Shi kadanSa.

Ya ku mutane! Ku saurari maganata, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa tare da ku a wannan wuri ba, kuma ba zan yi Hajji ba a bayan wannan shekara tawa.

Yaku mutane! Lallai Allah Madaukaki Yana cewa: “Ya ku mutane! Lallai ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabilu, domin ku san juna.

“Lallai mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafifincinku a takawa.”

Don haka Balarabe ba ya da fiffiko a kan Ba’ajame (wanda ba Balarabe ba), haka Ba’ajame ba ya da fiffiko a kan Balarabe, kuma baki ba ya da fiffiko a kan fari, fari ba ya da fiffiko a kan baki face fiffikon takawa.

Mutane dukkansu daga Adamu suke kuma Adamu daga turbaya yake. Ku saurara duk wata da’awa ya alla ta jini ko dukiya na sanya ta a karkashin kafafuwana, face ta kula da Ka’aba da kuma shayar da mahajjata.

Ya ku jama’ar Kuraishawa! Kada ku yarda ku zo Ranar Lahira kuna dauke da nauyi a kan wuyanku, yayin da sauran mutane suke bayyana (a gaban Allah) da ladaddaki alhali ba zan amfanar da ku da komai ba daga Allah.

Ku saurara! Duk wani abu na al’amarin Jahiliyya na take shi a karkashin kafafuwana kuma batacce ne, kuma jinanen Jahiliyya batattu ne.

Kuma jini na farko da aka zubar daga cikin jinanenmu shi ne jinin Ibn Rabi’atu bin Haris, ya kasance an raine shi a zuriyar Bani Sa’ad sai Huzailu ya kashe shi.

Kuma ribar Jahiliyya batacciya ce, kuma ribar farko da aka sanya ta riba a tsakaninmu ita ce ribar Abbas bin Abdulmudallib, to lallai ita batacciya ce gaba daya.

Ya ku mutane! Lallai ne jininku da dukiyarku da mutuncinku ababen katangewa ne (haramun ne) a tsakaninku har ku riski Ubangijinku, kamar yadda wannan rana take da girma kuma kamar yadda wannan wata naku yake da girma a wannan gari naku mai girma.

Kuma lallai ne za ku riski Ubangijinku kuma zai tambaye ku a kan ayyukanku.

Ya ku mutane! Lallai kuna da hakki a kan matanku, kuma su ma suna da hakki a kanku.

Daga cikin hakkinku a kansu, akwai cewa kada wanda ba ku so ya kwanta a kan shimfidarku, kuma kada su zo da wata alfasha bayyananniya, idan suka aikata haka, to, hakika Allah Ya yi muku izini ku kaurace musu a wuraren kwanciya kuma ku buge su duka wanda ba zai jawo rauni ba, idan suka hanu, to suna da hakkin ciyarwa da tufatarwa a kanku bisa alheri.

Ku saurara! Ba ya halatta ga mace ta bayar da wani abu daga dukiyar mijinta face da izininsa. Ku kula da mata wajen kyautata musu, domin su mataimakanku ne, ba su mallaka wa kansu komai.

Ku ji tsoron Allah a cikin al’amarin mata, domin kun karbe su ne da amanar Allah, kuka halatta farjojinsu da kalmomin Allah!

Ya ku mutane! Lallai ne Allah Madaukaki Ya bai wa kowane ma’abucin hakki hakkinsa, don haka babu wasiyya ga mai cin gado.

Kuma da na shimfidar aure ne, duk wanda ya keta dokar aure (ya yi zina) za a jefe shi.

Kuma hisabinsu yana ga Allah. Duk wanda ya jingina sunansa zuwa ga wanin mahaifinsa ko ya jingina kansa ga wanin wanda ya mallake shi (a tsakanin bayi), to la’anar Allah ta tabbata a gare shi. Wajibi ne a biya bashi, kuma a mayar da rance a saka wa kyauta, kuma wanda ya yi beli a dora masa asara.

Ku saurara! Babu wanda zai aikata babban laifi face (sakamakon) laifin yana kansa.

Mahaifi ba zai dauki laifin dansa ba, kamar yadda da ba zai dauki laifin mahaifinsa ba. Ba ya halatta ga mutum ya ci dukiyar dan uwansa face abin da ya ba shi bisa dadin rai daga cikinta, don haka kada ku zalunci kawunanku.

Ya ku mutane! Dukkan Musulmi dan uwan Musulmi ne, kuma lallai ne Musulmi ’yan uwan juna ne, bayinku, bayinku ne, don haka ku ciyar da su daga cikin abin da kuke ci, kuma ku tufatar da su daga cikin abin da kuke sanyawa.

Ku saurara! Kada ku koma batattu a bayana, sashinku yana dukkan wuyan sashi (kisan juna), kuma duk wanda ya zamo akwai wata amana a hannunusa, to, ya mayar da ita ga wanda ya ba shi amanar.

Ya ku mutane! Ku saurara kuma ku yi da’a ga wanda aka shugabantar da shi a kanku, koda kuwa bakin bawa mummuna ne daga Habasha aka shugabantar yana jagorantarku da Littafin Allah, to, ku saurara masa ku yi masa da’a.

Ya ku mutane! Lallai ne shi, babu wani Annabi a bayana, kuma babu wata al’umma a bayanku. Kuma hakika na bar muku abin da in kuka rike shi ba za ku bace ba a bayansa, idan kuka yi riko da shi: ‘Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa.’

Kuma ina yi muku kashedi a kan zufafawa (tsaurarawa da wuce-gona da iri) a cikin addini, domin wadanda suke gabaninku sun hallaka ne saboda zurfafawarsu a cikin addini.

Kuma lallai ne Shaidan, ya yanke kauna daga addininku, cewa za a bauta masa a wannan kasa taku har abada, amma zai kasance ana yi masa da’a a cikin ’yan abubuwan da kuke raina su na daga ayyukanku, sai ya yarda da su, don haka ku tsare addininku.

Ku saurara! Ku bauta wa Uabngijinku, ku yi sallolinku biyar, ku azumci watanku (na Ramadan) ku bayar da zakkar dukiyarku kuna masu tsarkake kawunanku da ita, kuma ku yi Hajjin Dakin Ubangijinku. Ku yi da’a ga ma’abuta al’amarinku (shugabanni) sai ku shiga Aljannar Ubangijinku.

Ku saurara! Wanda yake halarci (nan) ya isar ga wanda ba ya nan, domin da yawa wanda ake isar masa ya fi kiyayewa daga wanda ya ji. Kuma za a tambaye ku game da ni, to me za ku ce?”

Sai suka ce: “Mun shaida lallai ne kai ka bayar da amana, kuma ka isar da sakon kuma ka yi nasiha.”

Sai Manzon Allah (SAW) ya daga yatsarsa manuniya zuwa sama ya kuma dawo da ita zuwa ga mutane, ya ce: Ya Ubangiji! Ka zamo shaida. Ya Ubangiji! Ka zamo shaida (a gare ni, cewa na isar da aikenKa zuwa gabayinKa.”

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana kammala wannan Huduba, yana kokarin sauka daga Arfa sai aya ta sauka cewa:

“A yau Na kammala muku addininku, kuma Na cika ni’imaTa a kanku kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku…” (K:5:3).

An samo wannan Huduba ce daga littafin “THREE IMPORTANT ADDRESSES OF THE HOLY PROPHET (SAW), wallafar Sashin Da’awa da Shiryarwa na Cibiyar Binciken Musulunci (Islamic Research Institute) da ke Islamabad, Pakistan.