HUdUBA TA FARKO

Hadarin kafirta Musulmi (1) Daga Hudubar Imam Muhammad Murtada Gusau, Masallacin Nagazi-Ubete, Okene Jihar KogiMUkADDIMA:Bayan haka, ya bayin Allah! daya daga cikin miyagun ayyuka da suka saba wa Musulunci kuma suke aukuwa a tsakanin al’ummar Musulmi a yanzu shi ne dabi’ar nan ta kafirta Musulmi.  A cikin Hadisa da dama Manzon Allah (SAW) da kuma […]

HUdUBA TA FARKO
HUdUBA TA FARKO

Hadarin kafirta Musulmi (1)

Daga Hudubar Imam Muhammad Murtada Gusau, Masallacin Nagazi-Ubete, Okene Jihar Kogi
MUkADDIMA:
Bayan haka, ya bayin Allah! daya daga cikin miyagun ayyuka da suka saba wa Musulunci kuma suke aukuwa a tsakanin al’ummar Musulmi a yanzu shi ne dabi’ar nan ta kafirta Musulmi.  A cikin Hadisa da dama Manzon Allah (SAW) da kuma sahabbansa sun gargade mu a kan munin kafirta Musulmi ko jingina shi ga kafirci da shirka.
Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Duk lokacin da wani mutum ya ce wa dan uwansa kafiri, to sai Kalmar ta fada a kan dayansu,” (Buhari Hadisi na 5,753). Kuma Abu Huraira ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan wani mutum y ace wa dan uwansa ya kai kafiri, to za ta fada a kan dayansu.” (Buhari, Hadisi na 5,752).
Abu Zarri (RA) ya ruwaito cewa: “Maznzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wani mutumin da zai zargi wani da mugunta ko rashin imani face ta dawo a kansa idan abokin maganarsa barrantacce ne.” (Buhari, Hadisi na 5,698).
kaisu ya ruwaito Ibn Mas’ud (RA) yana cewa: “Duk lokacin da wani mutum ya ce da dan uwansa: Kai makiyina ne. To daya daga cikinsu ya bar Musulunci ko dan uwan nasa barrantacce ne.” (Adabul Mufrad: shafi na 421).
Domin haka, duk Musulmin da ya jefi dan uwansa da kalmar kafirci ko shirka da saninsa, to ya shirya daukar nauyin wannan kalma ta kafirci a Ranar kiyama.
’Yan uwa! Matsalar fitarwa daga Musulunci ko jifar wani daga kafirci matsala ce take bukatar nazari da daddalewa, amma sai wasu miyagu suke amfani da ita domin tayar da zaune-tsaye.
Sanannen abu ne cewa ran kowane Musulmi (da marar laifi da ba Musulmi ba) katangagge ne da ya zama wajibi kowa ya mutunta shi.
Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Musulmi katangagge ne ga kowane Musulmi: Kada a kashe shi kada a taba dukiyarsa kada a ci mutuncinsa.” (Muslim, Hadisi na 2564).
Don haha duk wanda ya kashe mumini ko Musulmi daya (ko duk wani mutum marar laifi) da gangan zai shiga wutar Jahannama kuma ya tabbata a cikinta. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la’ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma.” (k:4:93).
Haka rayukan wadanda ba Musulmi ba da suke zaune da Musulmi cikin lumana da zaman lafiya katangaggu ne, duk wanda ya kashe wani daga cikinsu da ganganci ba zai shiga Aljanna ba. Abdullah ibn Amru (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya kashe wani mutum da  yarjejeniyar zaman lafiya ta yi masa kariya, ba zai dandani kanshin Aljanna ba. Alhali hakika ana jin kanshin Aljanna a nisan tafiya shekarar arba’in.” (Buhari, Hadisi na 6516).
’Yan uwana masu girma! Domin kauce wa wadannan nassoshi na haramce-haramce, miyagun masu kafirta mutane daga cikin Musulmi sun kikrkiro wasu nazarce-nazarce da akidu na fitar da mutane daga Musulunci.  Khawarijawa ne suka fara kirkiro wadannan tatsuniyoyi kuma wannan muguwar koyarwa tasu tana ci gaba a yanzu a salon daukar makamai ana ta’addanci.
A gaskiya wadanda suke bayyana Musulmi da cewa ba Musulmi ko masu imani ba ne, kuma suke yi musu ta’addanci sun fi kusa da kafirci daga wadanda suke zargi.
Huzaifa (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika abin da nake ji musu tsoro shi ne mutumin da zai karanta Alkur’ani karatu mai dadi, amma yana jin haushin Musulunci sai ya canja abin da Allah Ya umarce shi, sai ya sabe daga gare shi (Alkur’anin) ya yi watsi da shi a bayan bayansa, ya rika cutar da makwabcinsa da makami ya rika zarginsa da kafirci.” Sai n ace “Ya Annabin Allah! Wanne ne daga cikinsu ya fi kusanci da kafirci? Wanda ake zargi ko mai zargin?” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Wanda yake zargin.” (Sahih Ibn Hibban, 81).
Allah Ya san wadansu Musulmi za su rika zargin wadansu da rashin imani su ki amincewa da bukatarsu ta zaman lafiya, saboda kawai suna son kawasar ganimar dukiyarsu. Don haka ne Allah Ya haramta haka, hani mai karfi.
Ibn Abbas ya ruwaito cewa:  “Wani mutum ya wuce ta wurin wani rukuni na sahabban Manzon Allah (SAW) tare da tumakinsa. Sai ya yi musu sallama, sai suka ce, “ya yi musu sallama ne don yak are kansa (suna shakkar Musuluncinsa).” Sai suka kai masa hari suka kashe shi suka dauki tumakin nasa. Suka je suka samu Annabi (SAW), sai Allah Ya saukar da ayar: “Yak u wadanda suka yi imani! Idan kun tafiya (a cikin kasa), domin jihadi, to ku nemi bayani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jefa sallama gare ku “ba Musulmi kake ba.” (k:4:94) a duba Sunan Tirmizi, Hadisi na 3030.
Ya bayin Allah! Masu kafirta mutane suna amfani da wannan dama ne ta raba mutane da imani ne domin su kwace dukiyar mutranen da ba su da laifi. Kuma sabanin haka, a Musulunci kashe ran Musulmi daya ya fi muni fiye da kyale mushirikai dubu su rayu.
Imam Al-Ghazali (Rahimahullah) ya ce: “Bincike domin a kan imanin mutum domin a samu uzurin kashe wani babban kuskure ne. Kuskuren kyale dubban (wadanda ba Musulmi ba da suke da hadari) su tsira ya fi sauki a kan zubar da jinin Musulmi daya.” Fathul Bari, mujalladi na 12 shafi na 314.
Wannan game da kuskuren kashe Musulmi daya da ake zargi da aikata shirka ne, To yaya girman laifin zai kasance a ce an ayyana gari ko birni ko kasashe ko daukacin jama’a da suke cike da Musulmi a ce su ba Musulmi ba ne?  wannan shi ne abin takaicin da muke fama da shi a yanzu, inda ake ayyana daukacin kasa da Musulmin da ke cikinta a matsayin kafirai ana aikata miyagun ta’addanci a kansu.
Taka-tsantsan da za mu yi a cikin wannan lamari zai dada fitowa fili ne idan muka fahimci muhimmin bambancin da ke tsakanin aikata kafirci da su kansu kafiran. Musulmi yana iya aikata aiki na kafirci saboda jahilci ko tawili, amma duk da haka Allah Yana iya daukarsu a matsayin Musulmi. Misalin wannan ya zo a cikin Hadisi mai zuwa:
Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wani mutum ya yi ta aikata zunubi, lokacin da mutuwa ta zo masa sai ya tara  ’ya’yansa ya ce: “idan na mutu, ku kone ni ku mayar da ni toka, sannan ku watsa a cikin teku, in gani ko Allah zai iya yi min azaba. Azabar da bai taba yi wa wani ba. Sai suka yi haka, a lokacin da ya bayyana a gaban Ubangijinsa, sai Ya ce masa: “Me ya sa ka yi haka?” Sai mutumin ya ce: “Tsoro da fargabar haduwa da kai ya Ubangiji! Sai Allah Ya gafarta masa saboda wannan.” (Muslim, Hadisi na 2756).