Hukuma ta jajanta wa iyalan alhazan da suka rasu a Saudiyya

Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kaduna ta aika da kwamitin mutum biyar zuwa gidajen alhazan jihar da suka rasu a yayin gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya. Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi.  […]

Hukuma ta jajanta wa iyalan alhazan da suka rasu a Saudiyya

Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kaduna ta aika da kwamitin mutum biyar zuwa gidajen alhazan jihar da suka rasu a yayin gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi. 

Sanarwar ta bayyana sunayen alhazan da suka rasu kamar haka, Abdulwahab Tukur da Warisu Abdullahi da Ya’u Sulaiman sai kuma dayyibat Isa (Keftin). Sun kuma fito ne daga kananan hukumomin Makarfi da Soba da Birnin Gwari da Kaduna ta Arewa.

Da yake jajanta wa iyalan mamatan da kuma jama’ar kananan hukumomin da duka fito, shugaba mai kula da hukumar jin dadin alhazan jihar, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansu hukurin jure wannan rashi da suka yi na ’yan uwan nasu.

Kwamitin, wanda shugaban tsare-tsare na hukumar ya jagoranta, Lawal Yakubu Ikara ya mika jakunkuna da kudaden mamatan ga ’yan uwansu.