Hukuma ta sake kama matar da ke yawon bara da ’ya’yanta biyu a Abuja
Hukumar Kare Muhalli ta Birnin Tarayya Abuja ta sake kama matar nan da ke yawon bara da ’ya’yanta mai suna Bilki Yahaya bayan a baya an kama ta kan wannan laifi. Matar mai suna Bilki Yahaya wadda ’yar asalin karamar Hukumar dandume a Jihar Katsina, Aminiya ta taba kawo labarin kama ta a kan irin […]

Hukumar Kare Muhalli ta Birnin Tarayya Abuja ta sake kama matar nan da ke yawon bara da ’ya’yanta mai suna Bilki Yahaya bayan a baya an kama ta kan wannan laifi.
Matar mai suna Bilki Yahaya wadda ’yar asalin karamar Hukumar dandume a Jihar Katsina, Aminiya ta taba kawo labarin kama ta a kan irin wannan matsalar a baya, daga bisani aka sake ta; a yayin da ’ya’yanta biyu, Abdurrahman Hamza mai shekara 6 da Ibrahim Hamza mai shekara 4 aka saka su a wata makaranta. An mika mata yaran bayan wasu watanni, bayan korafin da ta yi a jaridar Aminiya, cewa tana fuskantar musgunawa daga dangin uban yaran kan zargin ta sayar da su.
A zantawar da ta yi da wakilinmu a cibiyar koyar da sana’o’i ga nakasassu da ke kauyen Kuchiko-Abuja, ta ce, jami’an duba-gari sun kama ta ce tare da wadansu mutum 30 a ranar Lahadin da ta gabata a dandalin taro da ke Abuja, inda ta ce sun je don amsar tallafi daga wajen wani mai suna Abdurra’uf da ke raba taimakon Naira dubu 100 ga mata gwagware da kuma sauran al’umma da ke fama da nakasa, don kama sana’a da kuma kula da karatun yara.
Ta ce ba ta kai ga samun tallafin ba sai jami’an suka kama su.
Da aka tambaye ta ko ina labarin daya dan nata mai suna Abdurrahman, ta ce shi yana gida dandume yana zuwa makarantar Islamiyyya. Ta ce ba ta dawo Abuja da nufin yin bara ba sai dai don karbar taimakon wanda ta gani a talabijin ana rabawa.
A bayanin da ya yi wa Aminiya, shugaban cibiyar Kwamred Bala dantsoho ya ce ya yi nadamar ganin halin da matar ta sake jefa yaranta a ciki, bayan a baya ta yi alkawarin kiyaye hakan sannan za ta sanya su a makaranta. “A wancan karo wani ne ya dauki nauyin ’ya’yanta a makaranta, suna samun karatu da kulawa mai kyau, sannan bayan ta yi korafin rashin ganinsu, an ba ta damar ziyartar su a duk wata guda ko kasa da haka. Mai girma Minista ya sa baki aka mika mata yaran bayan ta dauki alkawari amma dubi abin da ta sake aikatawa,” inji shi.
Shugaban cibiyar ya ce za a ci gaba da tsare ta a cibiyar tare da dan nata, har sai sun ji daga gwamnatin jiharta ko kuma wata hujja kwakkwara.