NAHCON ta dakatar da rabon kujeru ga kamfanonin jirgin yawo
Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta dakatar da rabon kujerun aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jiragen yawo da suka samu aikin jigilar maniyyata
Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a dakatar da rabon kujeru aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jirgin yawo 40 da suka yi nasarar samun aikin jigilar maniyyata.
NAHCON ta dakatar da rabon kujerun ne saboda korafe-korafen da zargin rashin adalci da wasu kamfanonin da ba su yi nasara ba ke yi.
Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce hukumar na sane da irin wadanna zarge-zarge daga wasu kamfanonin da ba su yi nasara a tantancewar da aka yi ba.
Don haka aka dakatar da akain na tsawon awa 48 masu zuwa, domin daukar matakin da ya dace, tabbatar da tsafta a aikin da kuma kare martabar kukumar.
- Taurarin Zamani: Abubakar Isah Dandago (Al-Yamalash)
- Uwa da jaririyarta sun mutu a hatsarin kwalekwale a Adamawa
Fatima Sanda ta ce shugaban Hukumar, Jalal Ahmad Arabi, ya ba da dama ga duk kamfanin da ke da sahihin korafi kan rashin dacewar wani daga cikin wadanda suka samu aikin, ya gabatar da hujjojinsa domin a dauki matakin da ya dace.
Ta bayar da tabbacin za a yi zuzzurfan bincike a kan duk zargin da aka gabatar a rubuce, domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kujerun.
Kakakin ta NAHCON ta kara da cewa duk da haka, duk kamfanin da aka samu ya yi wa nai kage, zai fuskanci hukunci.