Hukumar Alhazai ta horar da jami’ai a Neja
Hukumar Alhazai ta Jihar Neja ta horar da mutanen da za su horar da masu koyar da maniyyata Hajjin bana 75 da suka hada da jam’in kula da alhazai na kananan hukumomi, da malami daya da mace a matsayin daya daga cikin matakan da hukumar ke dauka domin samun nasarar aikin Hajji karbabbe. Shugaban Hukumar […]
Hukumar Alhazai ta Jihar Neja ta horar da mutanen da za su horar da masu koyar da maniyyata Hajjin bana 75 da suka hada da jam’in kula da alhazai na kananan hukumomi, da malami daya da mace a matsayin daya daga cikin matakan da hukumar ke dauka domin samun nasarar aikin Hajji karbabbe.
Shugaban Hukumar Mai shari’a Jibrin Ndatsu Ndajiwo ya shaida wa mahalarta taron muhimmancin isar da abin da aka horar ga fiye da maniyyata dubu uku da ake sa ran su sauke farali a daga jihar a bana. Sai Mai shari’a Jibrin Ndajiwo ya tunatar da mahalarta taron su nanata wa maniyyata muhimmancin neman ilimin aikin Hajji.
Da yake gabatar da kasidan a wurin taron Dokta Muhammad Usman wanda Darakta ne a Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Neja ya ce wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta da maniyyata su ne matsalar hawan jini da gyambon ciki da sauransu, inda wasu kan rasa tsayuwar Arfa wanda yake daya ne daga cikin rukunan aikin Hajji.
Dokta Usman ya nanata matsayinsu na ci gaba da amfani da na’urar tantance mata masu juna biyu da ke boye cikinsu don zuwa aikin Hajji.
Mataimakin Gwamnan Jihar kuma Amirul Hajji na bana Alhaji Ahmad Muhammad Ketso ya tabbatar wa hukumar cewa gwamnati za ta bayar da duk goyon bayan da maniyyatan za su yi fice kamar shekarun da suka gabata, har jihar ta samu takardun yabo daga Hukumar Hajji ta kasa.
Amirul Hajjin y ace sun samar wa maniyyatan jihar masauki mai kyau a kusa da Harami, inda ya bukaci maniyyatan su yi wa gwamnatin jihar da ta tarayya addu’o’in samun nasarar inganta walwala da tattalin arziki.