Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara karbar kudin ajiyar maniyyata
Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara karbar kudin adashin gata a wannan watan na Nuwamba da muke ciki. Shugaban hukumar, Imam Husaini Suleman Tsoho Ikara ne ya fadi haka a yayin zantawarsa da Aminiya a Zariya. Ya ce: “Ka san cewa mu ne muka fi kowace jiha a Najeriya yawan Alhazai a aikin […]

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara karbar kudin adashin gata a wannan watan na Nuwamba da muke ciki.
Shugaban hukumar, Imam Husaini Suleman Tsoho Ikara ne ya fadi haka a yayin zantawarsa da Aminiya a Zariya. Ya ce: “Ka san cewa mu ne muka fi kowace jiha a Najeriya yawan Alhazai a aikin Hajjin bana da ya gabata, domin mun tafi da Alhazai dubu shida da dari bakwai da goma sha uku kuma Alhamdu lillahi.
Mun samu nasara kwarai da gaske, duk da ba mu muka fara tashin Alhazai ba amma mun yi nasara domin an kai gaban da mun riga wadanda suka fara kwashe Alhazanmu. Haka ma a wajen dawowa, nan ma mun samu nasara, domin mun dawo da Alhazanmu kafin wasu jihohin; don haka mun gode wa Allah.”
Shugaban ya kara da cewa: “Duk da kasancewa kudin aikin Hajji jama’a suna ganin ya yi tsada saboda tashin Dala, shi kuma aikin Hajji kusan duk da Dala ake amfani domin kashi 95 na kudin da ake aiki da su Dala ne, inda Naira take amfani ba shi da yawa, domin harka ce da ta shafi kasashen waje.
To mun yi kokari mun wayar wa da Alhazanmu kai da kuma nuna masu muhimmancin aikin Hajji. Amma mu dayake mafi yawan Alhazanmu na Jihar Kaduna na bana, kaso mafi yawa manoma ne kuma an samu amfanin gona mai yawa kuma Allah Ya sa ma amfanin gonar daraja. Don haka manoma su ne mafiya yawan Alhazanmu.”
Ya bayyana abin da ya sa suka fara shiri, inda ya ce saboda hukumar Alhazai ta kasa ta yi taro da su, domin fara tunkarar shirin aikin Hajji na badi. “To tun daga wannan rana shirin aikin Hajji ya fara, mu ma yanzu mun fara namu tsarin.
Domin a wannan taro da muka je har an ba mu yawan kujerunmu na Jihar Kaduna, kafin nan gaba idan da bukatar kari mu sai mu kara. Domin bana, kujeru 6,332 aka ba mu, daga baya ne aka kara mana kujeru har aka kai 6,750 kuma mun yi nasarar yi wa Alhazai 6,70 hidima kuma a cikinsu mutane talatin ne ba su sami tafiya ba saboda wasu na da ciki, wasu sun mutu, wasu kuma su suka san abin da ya hana su zuwa.”