Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta fara karbar kudin kujerun Hajjin bana
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara karbar kudin kujerun tafiya aikin Hajjin bana a jihar.Wata takardar sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hanun Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Badamasi Nuhu Usman ta ce hukumar ta fara karbar kudin kujerun ne a ranar Litinin da ta gabata kuma za ta […]
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara karbar kudin kujerun tafiya aikin Hajjin bana a jihar.
Wata takardar sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hanun Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Badamasi Nuhu Usman ta ce hukumar ta fara karbar kudin kujerun ne a ranar Litinin da ta gabata kuma za ta ci gaba da karba har zuwa ranar 1 ga Afrilu mai zuwa.
Hukumar ta ce maniyyatan za su fara biyan Naira dubu 850 a matsayin kudin kafin Hukumar Hajji ta kasa ta fitar da kudin da ya kamata a biya.
Hukumar ta nemi maniyyata da su kai shaidar takardun biyan kudi na banki na Naira dubu 850 da kananan hotunansu guda 20 da kuma fasfo zuwa kananan hukumominsu na asali domin tantancewa kafin a ba su kujerun Hajjin.
Hukumar ta yi kira ga jama’a su bi hanyar da ta dace wajen neman kujerun Hajjin tare da yin taka-tsantan don guje wa yin hulda da mutanen da ba su da hannu a kan aikin Hajji a hukumance.