Hukumar Alhazan Abuja za ta rufe karbar kudin ajiya daga maniyyata

Shugaban Hukumar Kula Da Jin Dadin Alhazai na Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Bashir MNI, ya bayyana cewa daga karshen watan nan na Fabrairu ne hukumar za ta rufe asusun gata na maniyyata da ke son tafiya aikin Hajji a bana. Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan jami’ar hukumar tasu […]

Hukumar Alhazan Abuja za ta rufe karbar kudin ajiya daga maniyyata

Shugaban Hukumar Kula Da Jin Dadin Alhazai na Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Bashir MNI, ya bayyana cewa daga karshen watan nan na Fabrairu ne hukumar za ta rufe asusun gata na maniyyata da ke son tafiya aikin Hajji a bana.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan jami’ar hukumar tasu ta kai Hedikwatar Kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya. Ya bayyana cewa tun farko sun bude adashin ne ga maniyyata tun a watan Nuwamba da ya gabata, inda aka bukaci maniyyata su rika ba da ajiyar Naira dubu 300 sau uku, inda akalla ake bukatar kafin watanni uku maniyyaci zai aje Naira miliyan daya, alabashi idan Hukumar Alhazai ta kasa ta ayyana adadin kudin kujera, sai ya cika sauran. Ya ce daga watan Maris, kowane maniyyaci sai dai ya biya jimillar kudin gaba daya.

Game da shirye-shiryen hukumar tasa kuwa, shugaban ya ce tuni sun fara gudanar da ayyukan da suka dace, domin ganin cewa aikin Hajji bana ya gudana cikin lumana da kula da alhazansu na Abuja. Ya ce tuni suka fara tattalin masaukai masu kyau kuma wadanda suka dace a Saudiyya, domin kyautata jin dadin Alhazan nasu. “Ayyukanmu a tsanake muke gabatar da su, mukan maida hankali sosai wajen ingantawa da tattalin mahajjata, musamman wajen sama masu  masaukai masu kyau kuma kusa da Harami, mukan kula da tsaro da abincinsu. Haka kuma ta fannin kiwon lafiya  mukan kula da maniyyata sosai ta fuskar tantance lafiyarsu tare da yi masu alluran rigakafi da sauransu.” Inji shugaba Muhammad Bashir, a yayin da yake amsa tambayar wakilan Aminiya.

An tambaye shi cewa ko hukumarsu na samun matsalar maniyyata masu makalewa a Saudiyya ko kuma mata masu juna biyu da ke zuwa aikin Hajji? Sai ya bayyana cewa ba su cika samun irin wadannan matsaloli ba, saboda irin matakan da suke dauka na bincike sosai tun a nan gida Najeriya. Ta bangaren masu satar hanyar makalewa a kasa mai tsarki kuwa, ya ce suna da tsari mai kyau na tantance maniyyata, yadda suke gindaya sharadin cewa maniyyaci dole ne ya kawo wanda zai tsaya masa a matsayin shaida, yadda idan ma ya aikata wani abu ba daidai ba, shaidar nan nasa za a tuntuba, domin daukar matakin da ya dace.

A yayin ziyarar, Shugaban Hukumar ya zo ne tare da rakiyar manyan jami’an hukumar ta jin dadin Alhazai da suka hada da Malam Aliyu Usman da Malam Aminu Musa da Malam Muhammad Baba Bawa da Malam Baba Adamu Audu Muhammad da Malam Auwal Dogondaji da Hajiya Hassana Lawal da Hajiya Ummukultuhm Abdullahi da Hajiya Maryam Larai Adamu da Muhammad Lawal Aminu da sauransu.