Hukumar alhazan Jigawa ta mayar wa gwamnati bashin N3.4bn
Hukumar ta ce za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da gaskiya a ayyukanta.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, ta mayar wa gwamnatin jihar bashin Naira biliyan 3.4 da aka ba ta domin taimaka mata wajen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo ne, ya miƙa kuɗaɗen ga gwamnatin jihar bayan kammala biyan bashin domin ta samu damar tanadin kujerun Hajji ga maniyyatan jihar da wuri.
- An kama mtum 10 kan satar waya, shanu da safarar ƙwayoyi a Jigawa
- Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan ƙarar ɗan takarar APC a Gombe
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ta mayar da kuɗin gaba ɗaya ba tare da ragi ko ƙara komai ba.
Ta bayyana hakan a matsayin gaskiya, riƙon amana da kuma kyakkyawan kula da dukiyar jama’a.
Hukumar ta ce tallafin kuɗin da gwamnatin jihar ta bayar ya taimaka mata wajen cika wa’adin da hukumomin Saudiyya suka gindaya na tanadin kujerun Hajji.
Ta ƙara da cewa hakan ya taimaka wajen tabbatar da cewa maniyyatan Jigawa sun samu damar gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin sauƙi ba tare da wata matsala ba.
Yayin miƙa kuɗaɗen, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar da kuma ƙoƙarinsa na inganta hidimar alhazai a jihar.
Ya ce bashin da gwamnati ta bayar ya taimaka wajen kammala muhimman shirye-shiryen Hajji a kan lokaci.
Labbo, ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata tare da tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukanta.
Ya kuma ce hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta hidimomin da take yi wa maniyyata ta hanyar tsara ayyuka da wuri da kuma amfani da dukiyar jama’a cikin kulawa.