Hukumar Alhazan Najeriya ta ƙayyade kuɗin Hajjin bana
Akwai banbancin tsakanin kuɗin kujerar da maniyyatan Arewa da Kudu za su biya.
Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta tsayar da hakikanin kuɗin da maniyyatan bana za su biya domin sauke farali.
Hukumar ta ce maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya za su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.
- Yau take ranar zaɓen cike giɓi da raba gardama a jihohi 26 na Nijeriya
- An rufe coci saboda addabar maƙwabta da hayaniya a Oyo
Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Fatima Sanda Usara.
Tun da farko hukumar Alhazan ta buƙaci maniyyatan su biya naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin ajiya, karin fiye da naira miliyan 1.5 kan kuɗin kujerar da aka biya a bara.
Hukumar ta ce an samu ƙarin kuɗin aikin hajin ne sakamakon tashin farashin dala, wani babban al’amari da ke ci wa tattalin arzikin arzikin ƙasar tuwo a ƙwarya.
Haka kuma, sanarwar ta buƙaci maniyyatan su tabbatar da kammala biyan kuɗaɗensu daga ranar 12 ga watan Fabrairun da muke ciki zuwa ranar 29 ga watan, wanda shi ne wa’adin ƙarshe na karɓar kuɗin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da muka yi bankwana da shi ne hukumomin Saudiyya suka yi wa maniyyatan Najeriya ragin kuɗin Hajjin bana.
Bayanai sun ce Shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi ne ya nemo ragin ragin da aka yi wanda ya shafin kuɗin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai a Saudiyya.
Sanarwar da Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kuɗin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.
“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.