Hukumar Almajirai: Ayyukan da ke kasafi ba su shafe mu ba

Hukumar ta ce huruminta shi ne jagorantar aiwatar da ayyukan.

Hukumar Almajirai: Ayyukan da ke kasafi ba su shafe mu ba

Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Su Zuwa Makaranta ta Ƙasa (NCAOOSCE), ta bayyana cewa wasu ayyukan da aka sanya mata a cikin Kasafin Kuɗin shekarar 2026 ba sa cikin hurumin da dokar da ta kafa ta, ta tanada.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Nura Muhammad, ya fitar, ya ce ayyukan da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu ayyukan mazaɓun ‘yan Majalisar Tarayya ne.

Ya ɗora wa hukumar alhakin aiwatar da su ta hanyar Dokar Kasafin Kuɗi.

Hukumar ta ce wannan tsari ba sabon abu ba ne, domin ana ɗora wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati alhakin aiwatar da ayyukan mazaɓu da zarar an amince da su a cikin kasafin kuɗin ƙasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, duk da cewa hukumar ce za ta aiwatar da waɗannan ayyuka, hakan ba ya nufin an sauya hurumin da doka ta ba ta.

Ta ce babban aikinta shi ne jagorantar ƙoƙarin gwamnati na inganta ilimin almajirai da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana cewa ta samu nasarar tantancewa da yin rajistar sama da yara 700,000 da ba sa zuwa makaranta, tare da kafa cibiyoyin karatu 119 a sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma ta ce tana ci gaba da wayar da kan al’umma da haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa yara sun samu damar shiga makaranta.

A ƙarshe, hukumar ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa hurumin da doka ta ba ta, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ɗan Najeriya ya samu damar samun ingantaccen ilimi.