Hukumar Birnin Tarayya ta kwace filotin Kwankwaso a Maitama
Hukumar Yankin Birnin Tarayya (FCTA) ta kwace fulotin Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ke yankin masu kumbar susa na Maitama a Abuja, bisa zargin ya keta ka’ida.Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Ministan Abuja Sanata Bala Mohammed ya rufe ofishin tuntuba na gwamnatin Jihar Adamawa inda ake zargin ’ya’yan […]
Hukumar Yankin Birnin Tarayya (FCTA) ta kwace fulotin Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ke yankin masu kumbar susa na Maitama a Abuja, bisa zargin ya keta ka’ida.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Ministan Abuja Sanata Bala Mohammed ya rufe ofishin tuntuba na gwamnatin Jihar Adamawa inda ake zargin ’ya’yan sabuwar PDP suna gudanar da ayyukansu.
Tuni aka fara jingina kwace filin Gwamna Kwankwaso da takaddamar siyasa da ke tsakanin bangaren Shugaban kasa Jonathan da gwamnoni bakwai da ake wa lakabi da G7 .
Wata majiya ta kusa da sashin filaye da bunkasa gine-gine na Hukumar FCTA ta ce Kwankwaso ya sayi wani fili mai girman murabba’in mita 2,500 a yankin Maitama a lokacin sayar da gidajen gwamnati a gwamnatin Obasanjo da ta gabata. Kuma ya samu izinin ya hada da wani fili mai dausayi da ke kusa bisa sharadin ba zai yi gini a wurin da ya kara ba. Sai dai a cewar majiyar Gwamnan ya yi gini a wurin sabanin ka’ida da amfani da fili a Abuja.
Jami’in ya ce kwace filin ya sa yanzu sashin kula da raya kasa ba ya da wani zabi face ya rushe wannan gini a wurin da aka kara.
Lokacin da aka tuntubi Kakakin Ministan Abuja, Nosike Ogbuenyi don jin ta bakinsa kan lamarin ya tabbatar da kwace filin, inda ya kara da cewa: “Lamarin na harkar aiki ne ba ya da alaka da siyasa. Ba mu duban idanun mutane.”
Da aka tambaye shi ko wannan wani sabo shafi ne a fafatawar da ake yi tsakanin gwamnonin bakwai da suke neman hana Jonathan takara a zaben shekarar 2015, Mista Ogbuenyi ya fusata da tambayar inda ya bukaci a fada masa dalilin yin irin wannan tambaya.
Ba a samu jin ta bakinmasu magana da yawun Gwamna Kwankwaso ba, domin Daraktan Watsa Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan Malam Baba Halilu dantiye bai dauki waya ba a lokacin da aka kira shi a ranar Lahadi da dare. Kuma da aka aika masa sakon waya, sai ya amsa da cewa, “Ya tafi aikin Hajji.” Shi ma Mai taimakawa na musamman ka harkokin labarai Jafar Jafar da aka ce ya tafi aikin Hajji bai dauki waya ba lokacin da aka tuntube shi. Yayin da Kwamishinan Watsa Labarai Farfesa Umar Faruk Jibril ma bai dauki waya ba kuma bai amsa sakon tes da aka aika masa ba. Gwamna Kwakwaso yana Saudiyya bisa gayyatar mahukuntan Saudiyya don yin aikin Hajjin bana.