Hukumar DFID za ta gudanar da wasan kwaikwayon wayar da kan jama’a

Hukumar bayar da taimako ta gwamnatin Ingila (DFID) ta fito da shirin wayar da kan jama’a ta hanyar wasan kwaikwayo a dangane da sha’anin mulki da sanin hakki da hadaka wajen gudanar ayyukan hukumomi da na jama’ar gari da magance nuna wariya ga mata da nakasassu da inganta zamantakewa da kuma samar da abubuwan more […]

Hukumar DFID za ta gudanar da wasan kwaikwayon wayar da kan jama’a

Ibrahim Mandawari da Shehu Hassan Kano a yayin taronHukumar bayar da taimako ta gwamnatin Ingila (DFID) ta fito da shirin wayar da kan jama’a ta hanyar wasan kwaikwayo a dangane da sha’anin mulki da sanin hakki da hadaka wajen gudanar ayyukan hukumomi da na jama’ar gari da magance nuna wariya ga mata da nakasassu da inganta zamantakewa da kuma samar da abubuwan more rayuwa domin ci gaban al’umma.
A karkashin wannan shiri mai suna Moblizing for Debelopment a Turance, ko kuma M4D a takaice, za a gudanar da wasan kwaikwayo na na dabe don fadakarwa a unguwannin kananan hukumomin jihohin Kano da Jigawa da Katsina da kuma Kaduna.
Abdullahi Zakari wanda aka fi sani da Ligidi, ya ce kungiyar wasan kwaikwayonsu mai suna Tauraruwa Youth Awareness na daya daga cikin kungiyoyin da za su gudanar da wasan kwaikwayon, kuma tuni daya cikin kwararrun marubutan wasan kwaikwayo da shirin fina-finan Hausa ya rubuta wannan wasa, sun kuma dukufa wajen atisayensa a karkashin kulawar jami’an shirin M4D. Kuma ba da dadewa ba za su gabatar da shi ga jama’a a wani taron gangami da za a gudanar a Kano da kuma sauran jihohin da aka zaba don gudanar da wannan shiri.