Hukumar DPR ta rufe gidajen man fetur a Adamawa

Hukumar kula da gidajen  man fetur (DPR) ta rufe gidajen man fetur biyu; A.Y.T Nigeria Limited da A.M.M.T Nigeria Limited da kuma famfon man fetur daya a gidan man NNPC  a Jihar Adamawa. Kwantrolan hukumar na Jihar Adamawa da Taraba, Mohammed Alaku ya bayyana cewa an rufe wadannan gidajen man ne saboda tsuke kan famfo […]

Hukumar DPR ta rufe gidajen man fetur a Adamawa

Hukumar kula da gidajen  man fetur (DPR) ta rufe gidajen man fetur biyu; A.Y.T Nigeria Limited da A.M.M.T Nigeria Limited da kuma famfon man fetur daya a gidan man NNPC  a Jihar Adamawa.

Kwantrolan hukumar na Jihar Adamawa da Taraba, Mohammed Alaku ya bayyana cewa an rufe wadannan gidajen man ne saboda tsuke kan famfo domin ya rage shigar man tare da tsuga farashin mai  da kuma rashin cikakkun takardu na saye da sayarwa.

Mohammed ya bayyana cewa ya rufe gidan man fetur din A.Y.T da ke kan hanyar karamar Hukumar Yola maso Gabas, saboda rashin cikakkun takardun saye da sayarwa.

Ya ce dalilin da ya sa ya rufe gidan man fetur din A.M.M.T NIgeria Limited yana da alaka da irin canjin launin man fetur din da suke sayarwa, kuma hakan zai iya haifar da matsala ga motoci.

Alaku ya ce suna iya kokarin ganin cewa kowane gidan man fetur ana sayar da mai a kan farashin da gwamnati ta yarda da shi na Naira dari da arba’in da biyar  kowace lita guda.

Ya gargadi sauran gidajen man da su kiyayi matse kan famfon man fetur, domin duk wanda aka kama da yin hakan za a ci tararsa Naira dubu dari.

Ya kara da cewa matsalar man fetur ta yi sauki a Jihar Adamawa da Taraba, saboda manyan motoci arba’in aka shigo da su  wadannan jihohin, kuma gidajen mai goma sha uku na aiki a cikin Jihar Adamawa.

Wani wanda ya zo shan man fetur, Muhammad Bukar ya ce matsalar man fetur da sauki yanzu ba kamar bara ba, sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jinjina wa Hukumar DPR kan yadda take gudanar da ayyukanta.

Muhammad Alaku ya yi kira ga jama’a da su kara hakuri a irin halin da suka tsinci kansu, sannan su kai karar duk gidan man fetur din da suke zargin yake matse kan famfo ko kuma sayar da man fiye da Naira 145.

 

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50