Hukumar DSS ta gurfanar da Sambo Dasuki a kotu
Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta gurfanar da tsohon Mai ba Shugaban kasa Shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.Hukumar DSS ta bayyana gurfanar da Dasuki ne a wata sanarwa dauke da sanya wani jami’inta mai suna Mista Tony Opuiyo a ranar Litinin da ta […]
Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta gurfanar da tsohon Mai ba Shugaban kasa Shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.
Hukumar DSS ta bayyana gurfanar da Dasuki ne a wata sanarwa dauke da sanya wani jami’inta mai suna Mista Tony Opuiyo a ranar Litinin da ta gabata, sai dai sanarwar ba ta bayyana a wace kotu aka gurfanar da shi ba, balle alkalin da zai yi shari’ar. Kuma sanarwar ba ta ce komai kan ko Dasuki ya bayyana a gaban kotun ko a’a ba, ko kuma yaushe za a fara sauraron shari’ar.
Wasu manyan lauyoyin Najeriya biyu -Yusuf Ali (SAN) da Abeny Mohammed (SAN), sun shaida wa Aminiya a ranar Litinin da dare cewa idan aka tabbatar da laifin da ake zargi za a iya daure shi shekara biyu mafi karanci ko shekara 14 mafi tsanani.
Hukumar DSS ta binciki gidajen Sambo Dasuki a ranar 15 ga Yuli bayan da ta mamaye su na tsawon kwana daya, inda bayan hakan ta ce ta kama sababbin motoci masu tsada 12 ciki har da motoci masu sulke guda biyar da kuma dimbin bindigogi da harsasai.
Sanarwar ta Opuiyo ta ce: “Idan za ku iya tunawa a ranar 16 ga Yuli, 2015 Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta gudanar da bincike kan gidaje mallakar tsohon Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Tsaro Mohammed Sambo Dasuki (Kanar mai ritaya), a Abuja da Sakkwto. Wannan mataki ya zamo dole sakamakon bayanan sirri masu inganci da suke alakanta shi da yin wasu abubuwa da za su iya kawo barazana ga tsaron kasar nan. Kuma binciken ya jawo an gano dimbin bindigogi da harsasai da sauransu wadanda aka gudanar da bincike a kai.”
Sanarwar ta kara da cewa “A ranar Litinin 24 ga Agusta, 2015, an gabatar da shi a gaban kotu bisa shaidun da aka gano, wadanda suka shafi nallakar bindigogi ba tare da lasisi ba, da za a iya hukunci a karkashin sashi na 27 (i) (a) (i) na dokokin mallakar bindigogi mai lamba Act Cap F28 LFN ta shekarar 2004. Wannan saboda bin hanyar dimokuradiyya ne da kudirinmu na bin doka da oda wajen tabbatar da babu wanda ya fi karfin doka komai matsayinsa a cikin al’umma. Don haka muna sanar da jama’a inda aka kwana a kan batun.”
Sanarwar ta bayyana kudirin hukumar na sadaukar da kanta wajen sauke nauyin da ke kanta na tabbatar da tsaro ga daukacin ’yan Najeriya domin ba su damar neman halalinsu tare da gudanar da rayuwarsu ta halattacciyar hanya.
Sai hukumar ta ce za ta shaida wa jama’a inda aka kwana a nan gaba.