Hukumar EFCC na bincike kan wani otel a Kaduna

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC tana bincike kan wani otel da ke mai Lamba 29a, aTitin Rabah da ke Kaduna, wanda ake zargin tsohon Mai ba Shugaban kasa Shawara a kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki da mallaka.Aminiya ta ziyarci otel xin inda ta ga an rubuta “EFCC tana gudanar da bincike. […]

Hukumar EFCC na bincike kan wani otel a Kaduna
Hukumar EFCC na bincike kan wani otel a Kaduna

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC tana bincike kan wani otel da ke mai Lamba 29a, aTitin Rabah da ke Kaduna, wanda ake zargin tsohon Mai ba Shugaban kasa Shawara a kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki da mallaka.
Aminiya ta ziyarci otel xin inda ta ga an rubuta “EFCC tana gudanar da bincike. A kiyayi wannan wuri,” a jikin ginin otel xin.
Otel xin wanda a da aka ce na wani tsohon xan kasuwa ne, ana zargin cewa Sambo Dasuki ne ya saye shi inda ake ta kawata shi da sauya masa fasali don ya dace da zamani.
Ginin otel xin yana rufe lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin.
Akwai wuraren da ake zargin ana bincike a kansu a garin Kaduna amma ba a rubuta alamar hukumar EFCC a jikinsu ba. Wuraren sun haxa da wurin sayar da sababbin motoci da sababbin gine-ginen shagunan alfarma.