Hukumar EFCC ta cafke barawon ATM

Hukumar yaki da masu  yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi katarin cafke wani matashi mai matsakaicin shekaru, mai suna Kingsley Mudi da ake zargin ya kware wajen yin amfani da katin debi-da-kanka (ATM) na jabu yana yi wa masu ajiyar kudi sata a asusunsu na banki.Cikin sanarwar da mai magana da […]

Hukumar EFCC ta cafke barawon ATM

Kingsley Mudi ke nan da kuma wasu daga cikin kayayyakin da aka same shi da su Hukumar yaki da masu  yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi katarin cafke wani matashi mai matsakaicin shekaru, mai suna Kingsley Mudi da ake zargin ya kware wajen yin amfani da katin debi-da-kanka (ATM) na jabu yana yi wa masu ajiyar kudi sata a asusunsu na banki.
Cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujare ya raba wa manema labarai ya ce rana ta baci ga Mudi ne yayin da wata majiya ta kyankyasa wa hukumarsu ta’annatin da matashin ya saba yi, suka baza komarsu suka yi katarin kama shi a harabar bankin Fidelity da ke Warri a Jihar Delta.
Sanarwar ta ce a yayin da aka kama shi, an same shi da katunan ATM talatin na bankuna daban-daban da ya yi amfani da su ya cire kimanin Naira dubu dari biyar da hamsin. Haka kuma an samu wasu cekin banki da aka sanya musu hannu na bankin UBA har guda takwas mallakar wasu mutane da ba a san ko su waye ba.
Matashin ya bayyana wa EFCC cewa shi wanzancin zamani yake yi a wani shagonsa kuma ya ce wani lokaci shi mawaki ne wato marokin baki.
Kakakin hukumar ya ce da zarar sun gama bincike a kansa za su gurfanar da shi gaban kuliya, ba tare da wani jinkiri ba.