Hukumar EFCC ta gano Naira miliyan 65.5 a ofishin INEC

A wani samame da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kai  ta ce ta bankado fiye da Naira miliyan 65.5 a ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Jihar Zamfara. Hukumar EFCC ta sanar da cewa ta samu kudin ne a cikin wasu akwatunan adana kudi masu sulke a ofishin akanta da […]

Hukumar EFCC ta gano Naira miliyan 65.5 a ofishin INEC

Dakataccen Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

A wani samame da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kai  ta ce ta bankado fiye da Naira miliyan 65.5 a ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Jihar Zamfara.

Hukumar EFCC ta sanar da cewa ta samu kudin ne a cikin wasu akwatunan adana kudi masu sulke a ofishin akanta da mai kula da kudin Hukumar INEC a Jihar.

Kudin dai sun hada da bandir-bandir din Naira dubu-duba guda 81 da bandir 97 na Naira  dari biyar-biyar da kuma Naira 500 guda 96, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Bayanin wanda ya fito daga Hukumar EFCC shiyyar  Sakkwato wadda ta jagoranci kai samamen ta ce ta samu korafi ne daga wani ma’aikacin wucin-gadi na Hukumar INEC da ya yi aikin zaben bana a jihar amma ba a biya shi hakkinsa ba. Ma’aikacin ya yi zargin cewa ba su samu alawus na Naira 6000 na aikin zabe da suka yi guda biyu ba.

Hukumar EFCC ta ce tana zargin kudin na daga cikin kudaden da gwamnati ta saki ga Hukumar INEC domin yin aron kujeru da rumfunan zabe sannan kuma a biya ma’aikata.

Har zuwa rubuta wannan rahoto Hukumar INEC ta Kasa ko ta Jihar Zamfara ba su ce uffan ba dangane da batun wadannan kudi da Hukumar EFCC ta ce ta kama a ofishinsu na Zamfara.