Hukumar EFCC ta garkame gidan Maina

Mai Magana da Yawun Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya fada wa Aminiya cewa har yanzu sunan Maina yana cikin jerin sunayen da hukumar ke nema ruwa a jallo. Ya ce tuni Hukumar EFCC ta mika koke ga ma’aikatar cikin gida tana mai sanar da ita zarge-zargen da ake yi masa tun kafin labarin korarsa daga […]

Hukumar EFCC ta garkame gidan Maina

Mai Magana da Yawun Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya fada wa Aminiya cewa har yanzu sunan Maina yana cikin jerin sunayen da hukumar ke nema ruwa a jallo.
Ya ce tuni Hukumar EFCC ta mika koke ga ma’aikatar cikin gida tana mai sanar da ita zarge-zargen da ake yi masa tun kafin labarin korarsa daga aiki ya bayyana.
Hukumar EFCC ta kai simame gidansa inda ta rufe gidan mallakar Maina wanda ke lamba 10 kan titin Amisi Musa da ke Jabi Abuja.