Hukumar EFCC za ta tsare Fani-Kayode na mako biyu
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), ta samu izinin kotu na tsare tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Cif Femi Fani-Kayode, bisa zarginsa da hannu a cire Naira biliyan biyu da rabi daga Babban Bankin Najeriya ta haramtacciyar hanya inda aka sanya a asusun jiga-jigan PDP shida da kuma wata kungiyar magoya bayan […]
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), ta samu izinin kotu na tsare tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Cif Femi Fani-Kayode, bisa zarginsa da hannu a cire Naira biliyan biyu da rabi daga Babban Bankin Najeriya ta haramtacciyar hanya inda aka sanya a asusun jiga-jigan PDP shida da kuma wata kungiyar magoya bayan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna Goodluck Support Group (GSG).
Ana zargin Fani-Kayode ya samu Naira miliyan 840 daga cikin kudin wadanda aka tura domin gudanar da kamfe din tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a bara.
Wannan izini ne ya zo ne a wuni na biyu da Hukumar EFCC take yi wa tsohon Ministan tambayoyi, inda ake sa ran hukumar za ta tsare shin a tsawon mako biyu, kuma a iya sabunta hakan idan EFCC tana da hujja mai karfi na a ci gaba da tsare shi.
Wata majiya ta ce hukumar ta samu izinin ne daga wata Kotun Majistare domin ta ci gaba da tsare Fani-Kayode a daidai lokacin da ake ci gaba da bincikarsa kamar yadda sashi na 293 (1) na dokar gudanar da shari’ar manyan laifuffuka nta shekarar 2015.
Hukumar EFCC ta ce Naira biliyan biyu da rabin da ake magana an raba ne kamar haka:
Fani-Kayode (ya samu Naira miliyan 840); Goodluck Support Group (Naira miliyan 320); Achike Udenwa da biola Onwuliri (Naira miliyan 350); Nenadi Usman (Naira miliyan 140); Olu Falae (Naira miliyan 100) da Okey Ezenwa (Naira miliyan 100). Kuma daga cikin mutum shida da ake zargi da hannu a badakalar, Hukumar EFCC ta riga ta yi tambayoyi ga wadansu tsofaffin jami’an gwamnati uku da sukia hada da tsohuwar Minista a Ma’aikatar Kudi Misis Nenadi Usman da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Achike Udenwa da kuma Fani-Kayode.
Ana zargin an biya Fani-Kayode adadin Naira miliyan 840 a kashi uku zuwa asusunsa.
Wata majiya ta ce, biya na farko an tura masa Naira miliyan 350 cikin asusunsa a ranar 19 ga Fabrairun bara, sai Naira miliyan 250 da ita ma aka biya a ranar 19 ga Fabrairun na bara, yayain da aka tura masa Naira miliyan 240 daga baya wato ranar 19 ga Maris din bara.
Kuma jimillar kudin da yake cikin asusun zuwa ranar 31 ga Disamban bara shi ne Naira miliyan 189 da dubu 402 da 72.
Shi kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cif Olu Falae ana zargin ya karbi Naira miliyan 100 ta hannun kamfanin Marreco Limited, kamfanin das hi ne shugabansa.
An shigar da kudin ne ta asusun kamfanin da ke bankin United Bank for Africa Plc, Mai lamba1000627022 a ranar 25 ga Maris din shekarar 2014.
Majiyar ta kuma ce, Achike Udenwa da tsohuwar Minista biola Onwuliri, sun samu Naira miliyan 350 a lokuta biyu daban-daban. A biya na farko a tura musu Naira miliyan 150 ta asusun hadin gwiwarsu da ke bankin Zenith Bank a ranar 13 ga Janairun bara, sai biya na biyu aka tura musu Naira miliyan 200 a asusunsu da ke bankin Diamond Bank, yayin da ake zargin Okey Ezenwa da wawurar Naira miliyan 100.