Hukumar Fansho ta Jigawa ta biya iyalan ma’aikatan da suka rasu N288m
Daga watan Janairu zuwa Yulin 2026, an biya jimillar Naira biliyan 4 da miliyan 91 ga waɗanda suka yi ritaya da kuma iyalan mamata.
Hukumar Kula da Fansho ta Jiha da Ƙananan Hukumomin Jigawa ta fara biyan haƙƙoƙin iyalai 90 na ma’aikatan da suka rasu suna karɓar fansho har kimanin Naira miliyan 288.
Sakataren Zartarwa na hukumar, Dakta Bilyaminu Shitu, ne ya bayyana haka yayin ƙaddamar da shirin biyan kuɗaɗen a Dutse.
- Cece-ku-ce ya hana ni zama kocin Italiya — Andrea Pirlo
- Sarkin Bade ya jagoranci sallar roƙon ruwa a Yobe
Ya ce waɗanda za su amfana sun haɗa da iyalan ma’aikatan da suka rasu suna bakin aiki, da kuma iyalan waɗanda suka yi ritaya sannan suka rasu bayan sun fara karɓar fansho.
A cewarsa, wannan ne karo na huɗu da hukumar ke gudanar da irin wannan biyan kuɗaɗe a shekarar 2026, bayan waɗanda aka yi a watan Janairu, Fabrairu da Mayu.
Dakta Shitu ya ce daga cikin kuɗaɗen, Naira miliyan 261 za a biya iyalai 17 na ma’aikatan da suka rasu suna bakin aiki, yayin da kusan Naira miliyan 27 za a biya iyalan waɗanda suka yi ritaya sannan suka rasu kafin cikar wa’adin soma samun fanshonsu.
Ya ƙara da cewa a makon da ya gabata ma, hukumar ta biya waɗanda suka yi ritaya 453 haƙƙoƙinsu, lamarin da ya sa jimillar kuɗaɗen da aka fitar cikin makonni biyu ta kai kusan Naira biliyan 1 da miliyan 289.
A cewarsa, daga watan Janairu zuwa Yulin 2026, hukumar ta biya jimillar Naira biliyan 4 da miliyan 91 ga waɗanda suka yi ritaya da kuma iyalan mamata.
Ya ce kuɗaɗen za su amfanar da waɗanda suka yi ritaya kimanin 1,741, da iyalan ma’aikata 2,091 da suka rasu suna bakin aiki, da kuma iyalai 83 na waɗanda suka yi ritaya suka fara karɓar fansho sannan suka rasu.
Dakta Shitu ya danganta nasarar da hukumar ke samu wajen biyan haƙƙoƙi a kan lokaci da cikakken goyon bayan Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dakta Umar A. Namadi.
Ya ce duk lokacin da hukumar ta buƙaci kuɗaɗe domin biyan haƙƙoƙin waɗanda suka yi ritaya da iyalan mamata, gwamnatin jihar kan gaggauta amincewa da buƙatar.
Ya kuma yi kira ga waɗanda ke kula da iyalan mamatan da su yi amfani da kuɗaɗen a hanyoyin da suka dace, musamman wajen ilimantar da yara da inganta rayuwarsu.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun bayyana farin cikinsu, tare da yaba wa gwamnatin jihar bisa gaggauta biyan haƙƙoƙinsu.
Sun ce biyan kuɗaɗen a kan lokaci ya rage musu raɗaɗin rayuwa, ya kuma ba su damar kula da iyalansu da ci gaba da karatun yaran da mamatan suka bari.
Haka kuma, sun yi addu’ar Allah Ya saka wa gwamnatin jihar da alheri, tare da roƙon a ci gaba da wannan tsari domin tabbatar da cewa kowane mai haƙƙi yana samun nasa ba tare da wata tangarda ba