Hukumar FBI ta wanke Hillary Clinton
Hukumar Binciken Manyan Laifuka a Amurka (FBI) ta ce ba wani laifin da za a iya tuhumar wadda ake kyautata zaton za ta zama ’yar takarar jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton.Misis Clinton ta yi amfani da adireshin kashin kanta lokacin tana Sakatariyar Harkokin Wajen kasar Amurka. Matakin dai ya share mata duk wani shinge da ka […]

Hukumar Binciken Manyan Laifuka a Amurka (FBI) ta ce ba wani laifin da za a iya tuhumar wadda ake kyautata zaton za ta zama ’yar takarar jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton.
Misis Clinton ta yi amfani da adireshin kashin kanta lokacin tana Sakatariyar Harkokin Wajen kasar Amurka.
Matakin dai ya share mata duk wani shinge da ka iya zame mata alkakai domin samun damar tsayar da ita a matsayinn ’yar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Democrat.
Babban Daraktan FBI James Comey a ranar Talata ya ce Misis Cliton da abokan aikinta sun nuna halin ko in kula wajen tantance sakonnin da suka yi kewaya tsakamnin su ta kundin tattara bayanai na yanar gizo mallakarta.
Har ila yau, Comey ya ce binciken hukumar da aka kwashe tsawon mako guda suna gudanarwa sun kasa samun wata hujja mai karfi daga dubban sakonnin da ta aike da su, wanda ya nuna cewa ta karya dokar kasa, don haka ba wani mai binciken da zai ce ga abin da zai gabatar domin bayyana laifinta a kan amfani da wannan kundin tattara bayanai mallakarta.
Hukumar FBI ta gudanar da gagarumin bincike game da amfani da tayi da kundin tattara bayanai mallakar kanta madadin na gwamnati, inda suka kwashe sa’o’i uku da rabi suna mata tambayoyi a babban ofishin hukumar da ke birnin Washington DC.
Wadannan kalaman na Mista Comey sun zo ne mako daya bayan gutsiri tsoman da ake tayi lokacin da mijin Hillary Clinton wato tsohon Shugaba Bill Clinton ya gana da babban mai shari’a na kasa Loretta Lynch, wanda suka yi a tashar jirgin sama na Phonid da ke Jihar Arizona, sun kwashe minti 30 suna tattaunawa, amma kuma ba su tabo batun ba.
Sai dai abin da ya haifar da surutan game da wannan ganawar shi ne Loretta ita ce ta shugabanci binciken farko game da zargin da ake yi wa Hilary game da amfani da wannan kundin tattara bayanai.
’Yan jam’iyyar Republican da ’yan jam’iyyarsu ta Democrat musammam masu goyon bayan Bernie Sanders su ma sun soki wannan ganawar ta Bill Clinton da Loretta Lych.
Sai dai abokin hamayyarta na jam’iyyar Republican Donald Trump a wajen gangamin yakin neman zabensa a Jihar North Carolina, ya ce wadannan kalaman shugaban hukumar FBI abin kunya ne.
Trump ya ce “dama nasan cewa za ta tsallake wannan siradin.”
A mako mai zuwa ne dai za a yi babban taron jam’iyyar Republican wanda zai tabbatar ko Trump shi ne zai tsaya wa jam’iyyarsu takara a zaben shugaban kasa ko kuma a’a, a mako na gaba kuma a gudanar da na jam’iyyar Democrat.