Hukumar FIRS ta sauya salon karbar haraji
Hukumar Tara Kudin Shiga ta kasa (FIRS) ta sauya sabon salo don tara kudin shiga ta hanyar lika takardar gargadi kan tilas ne a biya kudin ciniki kashi biyar cikin 100.Takardar da Shugaban Hukumar ya rubuta tana da sako kamar haka: “Hukumar tara kudin shiga tana fito da sabbin dabarun tilastawa masu ofisoshin kamfanoni da […]
Hukumar Tara Kudin Shiga ta kasa (FIRS) ta sauya sabon salo don tara kudin shiga ta hanyar lika takardar gargadi kan tilas ne a biya kudin ciniki kashi biyar cikin 100.
Takardar da Shugaban Hukumar ya rubuta tana da sako kamar haka: “Hukumar tara kudin shiga tana fito da sabbin dabarun tilastawa masu ofisoshin kamfanoni da na kasuwanci don su rinka tattarawa da mika kudin shiga wato kashi biyar daga cikin na ababen alfarma wato bAT.”
Wani mai shago ya ce hakan ba zai hana alaka da shirin da hukumar ta yi ba na kara kwazo don karin nemo kudin shiga gadan-gadan domin wadansu basa son biyan kudin shiga ko kuma suna tarawa, amma ba sa mika wa gwmanati don ayi aikin ci gaban jama’a dungurungun.
Wakilinmu ya kewaye birnin Abuja inda ta ga an lika wadannan bayanai musamman ma a sabbin shagun alfarma.
Sakon ya kara da cewa Gargadi: “An lika wannan takarda ne domin mai wannan kamfani ko shago ya ki bin dokan tara kudin harajin na kayayyakin alfarma kamar yadda dokan Najeriya ta bayyana a kundin doka na shekarar 2004. Duk wanda ya karya wannan doka za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.” Bugu da kari akwai inda aka kewaye da jan layi wanda ya nuna cewa: “Kada wanda ya cire wannan takarda ba tare da izinin shugaban hukumar tara kudin shiga ta kasa ba.
Har ila yau, wandanda muka zanta da su wadanda aka lika musu wannan sako a wurarensu sun ki yarda su bayyana sunayensu, amma hakan bai hana su ci gaba da harkakinsu ba da tattaunawa na neman fahimtar juna ba kamar yadda ake yi a dab a na rufe wurin aikin gaba daya.