Hukumar FRSC ta bukaci hadin kan ’yan jarida wajen fadakar da direbobi

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadari ta kasa (FRSC) a Jihar Gombe Mista Ayobami Omiyale, ya bukaci hadin kan ’yan jarida a kokarin da hukumar ke yin a fadakar da direbobi illar mugun gudu a kan hanyoyin jihar.Kwamanda Omiyale ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga ofishin wakilan kafafen watsa labarai da ke […]

Hukumar FRSC ta bukaci hadin kan ’yan jarida wajen fadakar da direbobi
Hukumar FRSC ta bukaci hadin kan ’yan jarida wajen fadakar da direbobi

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadari ta kasa (FRSC) a Jihar Gombe Mista Ayobami Omiyale, ya bukaci hadin kan ’yan jarida a kokarin da hukumar ke yin a fadakar da direbobi illar mugun gudu a kan hanyoyin jihar.
Kwamanda Omiyale ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga ofishin wakilan kafafen watsa labarai da ke Gombe.
Mista Omiyale, ya ce a yanzu da ake kokarin fara shagulgulan Babbar Sallah da kuma watannin karshen shekara da aka fi samun aukuwar haddura a cikinsu akwai bukatar ’yan jarida su fadakar da direbobi illar mugun gudu domin kare rayuka da dukiyar jama’a.
Ya ce duk wata kungiya ko hukuma da ke son cimma burinta dole ta hada kai da ’yan jarida wajen cimma nasarar fadakar da jama’a.
Kwamandan ya ce a kullum hadarurruka na kara aukuwa a kan manyan hanyoyin kasar nan kuma a yanzu haka sun karu da kashi 80 cikin 100 don haka akwai bukatar a nemo hanyar rage su.
Ya ce za su gana da ’ya’yan kungiyar direbobin manya da kananan motoci don fadakar da su dokokin hanya da yadda za su rika kiyayewa saboda a rage aukuwar hadari a hanyoyin musamman a lokutan bukukuwan karshen shekara.
Ya ce yayin da gangancin direbobi ke jawo mafi yawan hadarin, rashin kyan hanyoyi na taimakawa wajen aukuwar hadarin.
Da yake maida jawabi shugaban kungiyar Mista Timothy Choji, ya jinjina wa Hukumar FRSC bisa wannan ziyara, kuma ya kiraye ta cewa ta rika shirya taron ganawa da ’yan jarida duk wata ko bayan wata uku-uku don sanar da ayyukan da take gudanarwa ta yadda hakan zai taimaika wajen wayar da kan al’umma.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi