Hukumar harajin Pakistan ta kai wa masu almubazzaranci a bikin auren farmaki
Wani ango a kasar Pakistan ya yi wa bakin da suka halarcin bikin aurensa ruwan Dalar Amurka da Riyal din Saudiyya, inda wannan biki na kasaita ya jefa shi cikin bala’i har ta kai ga Hukumar tara haraji ta tarayyar kasar na binciken yadda ya samu dukiyarsa. Hukumar harajin ta FBR ta ankara da almubazzarancin […]
Wani ango a kasar Pakistan ya yi wa bakin da suka halarcin bikin aurensa ruwan Dalar Amurka da Riyal din Saudiyya, inda wannan biki na kasaita ya jefa shi cikin bala’i har ta kai ga Hukumar tara haraji ta tarayyar kasar na binciken yadda ya samu dukiyarsa.
Hukumar harajin ta FBR ta ankara da almubazzarancin bikin ne, inda aka yi watsi da dukiya a birrnin Khanpur da ke lardin Punjab, yayin da iyayen ango suka yi ta watsi da kudaden kasar wajen, tare da jefa wa wadanda suka zo daurin auren sababbin wayoyin hannu.
Ango Mohammad Arshad, mazaunin yankin Shujabad da ke Multan, ya auri wata mata a binrin Khanpur, alamu sun nuna cewa ya yi iya yinsa dion tabbatar da cewa ba za a manta da wannan biki na kasaita da ya gudanar ba.
Da iyayen Arshad suka isa gidan su amarya, sai suka fara bayar da kyaututtuka na miliyoyin rupee (kidin Pakistan), tare da Dalar Amurka da Riyal din Saudiyya da sababbin wayoyin salula ga bakin da suka halarci bikin.
A bidiyon da akanuna an ga iyayen ango suna jefa kyaututtukan gabakin, wadanda su kuma suka yi ta tsallesuna cafewa. Dalabarin ya bazu, sai sauran mazauna birnin Khanpur suka yi ta durarowa zuwa wurin bikin don neman sa’ar samun rabonsu daga dimbin dukiyar da aka yi watsi da ita..Kusankowane mutum da ya halarci bikin ya samu rabonsa a ‘ruwan kudin’. Wasu sun yi sa’ar samun daloli, wasu kuwa sababbin wayoyin salula.
’Yan bikin sun ce angon yana da ’yan uwa takwas da ke zaune a Amurka, hudu daga cikinsu suna zaune a Saudiyya, al’amarin da ke tabbatar da yadda aka yi ya samu daloli da kudin Riyals na Saudiyya.
Almubazzaranci da watsi da dukiya a bukukuwan kasaita suke yi a kasar Pakistan, ta yadda ganin yadda lamarin ya zama ruwan dare sai gwamnati ta fara kai farmaki duk inda ake watsi da dukiya.
A wata Maris din bara, wani ango ya yi rawani da kanun yadi 50 da aka feshe da ruwan zinari (rawanin sehra na al’adar mutanen Pakistan), sannan ya gayyaci baki 15,000, ne da kwatsam sai hukumar haraji ta kai masa farmaki.
Sannan a Satumbar bara wwani angon ya yi amfani da karamin jirgin samadon sauka a wajen bikin aurensa na Sheikhapur, amma hukumar harajin ba ta samu kama shi ba.
An dai sha sukar lamairin bukukuwan da ake wadaka da dimbin dukiya a kasar Pakistan sabnoda suna kara nuna wawakeeken gibin da ke tsakanin talkaw ada attajiran kasar.
“Wannan almubazzarancin ba wai nuna bambanci tsakanin masu shi, madaukaka a cikin al’umma da marasa shi (talakawa) kawai yake yi ba, harma yana tursasa wasu su dabaibayen kansu da dimbin bashi don kawai su kambama kansu,” a cewar Saima Hameed, wata Farfesa kimiyyar nazarin halayyar dan Adam.