Hukumar HYPPADEC za ta fara aiki gadan-gadan – Sanata Umaru

Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas Sanata Dabid Umaru, ya ce nan ba da jimawa ba Hukumar Raya Yankunan da ke da Tashoshin Wutar Lantarki (HYPPADEC) za ta fara aiki gadan-gadan don bunkasa yankunan da tashohin wutar lantarkin ke cikinsu.Sanata Dabid Umaru ya bayyana haka ne yayin da ya kira wani taron manema labarai […]

Hukumar HYPPADEC za ta fara aiki gadan-gadan – Sanata Umaru
Hukumar HYPPADEC za ta fara aiki gadan-gadan – Sanata Umaru

Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas Sanata Dabid Umaru, ya ce nan ba da jimawa ba Hukumar Raya Yankunan da ke da Tashoshin Wutar Lantarki (HYPPADEC) za ta fara aiki gadan-gadan don bunkasa yankunan da tashohin wutar lantarkin ke cikinsu.
Sanata Dabid Umaru ya bayyana haka ne yayin da ya kira wani taron manema labarai don bayyana ayyukan da ya gudanar a Majalisar Dattawa a shekara daya, wanda ya gudana a ofishinsa da ke Mina a ranar Litinin da ta gabata.
Sanata Umaru ya ce kudirin da ya gabatar na a yi wa dokar Hukumar HYPPADEC gyaran fuska yana da alfanu sosai ga al’ummomin yankunan. Ya ce sai da ya rika lallamin abokan aikinsa a majalisa don su ba shi goyon baya tare da amincewa kudirin ya samu shiga ta yadda zai zama doka.
Sanatan ya ce tuni kudirin dokar ya tsallake mataki na farko inda ya bayar da tabbacin cewa zai tsallake mataki na biyu a zauren majalisar.
Ya ce ya samu nasarar ganin abokan aikinsa a majalisa sun amince da ware Naira miliyan 70 a cikin kasafin kudin bana wanda za a yi amfani da shi wajen kaddamar da hukumar.
Kuma ya ce a shekara dayan da ya yi a majalisa ya samu nasarori da yawa da suka hada da gabatar da kudirin doka biyar da gabatar da koke-koke uku da abubuwa masu yawa.
Sanatan wanda har ila yau shi ne Shugaban Kwamitin Shari’a da Kare Hakkin dan Adam a majalisar ya bayyana cewa daga cikin kudirorin dokar da ya gabatar akwai kudirin kafa hukumar da za ta rika tantance iyaka a tsakanin Jihar Neja da Birnin Tarayya, Abuja.
Ya ce ya kuma samar da na’urorin kara karfin wutar lantarki wato taransfoma a kauyukan da ke karkashin wakilcinsa da bayar da tallafi ga mutane masu yawa da ke fama da lalura iri-iri.